Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman tsarinsa daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta mawa sai Allah. Kuma ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.
Bayan haka, ya ku bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah, ku san irin mutane da za ku yi abota da su. Kuma ku lura da irin waxanda ’ya’yanku ke abota da su. Abokai suna da tasiri qwarai game da mutuncin mutum. Idan abokan mutum ba mutanen kirki ba ne, babu wanda zai yarda cewa shi muutumin kirki ne. Ku dubi yadda Alqur’ani ya bayyana mutuncin abokan (Sahabban) Annabi (SAW), kuma ya xauki matakai masu tsanani kan duk wanda yake neman y ace sub a mutanen kirki ba ne. Saboda hakan zai iya shafar Annabi (SAW). Sai Allah Ya ce: (Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai masu rahama ne a tsakaninsu. kana ganin su suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu da yardarSa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu daga kufan sujuda. Wannan shi ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma a cikin Linjila ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya qarfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan qafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) Ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa’adi ga waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan qwarai daga cikinsu da gafara da ijara mai girma.” (Q:48:29).
Kuma lokacin da munafuqai suka yi ta zargin sahabinsa Safwan bn Mu’addil da Uwar Muminai A’isha (RA) da aikata fasiqanci, sai Allah Ya saukar da ayoyin Alqur’ani domin kare su da kuma ladabtar da waxanda suka yi ta yaxa maganar. Shi kuma jagoran qulla wannan makirci, Allah Ya yi alqawarin sai Ya yi masa azaba. Sai Allah Ya ce: “Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma mmiyagun maza domi miyagun mata suke, kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke, kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. Waxancan su ne waxanda ake barrantawa daga abin da (masu qazafi) suke faxa, kuma suna da gafara da arziki na karimci.” (Q:24:26).
Kuma an ladabtar da waxanda suka wannan qazafi kamar haka: “A lokacin da kuke marabarsa da harsunanku kuma kuna cewa da bakunanku abin da ba ku da wani ilimi game da shi, kuma kuna zaton sa mai sauqi, alhali kuwa a wurin Allah, babba ne. Kuma don me a lokacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, “Ba ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan qiren qarya ne mai girma. Allah Yana yi muku wa’azi kada ku koma ga irinsa har abada, idan kun kasance muminai.” (Q:24:15-17).
Shi kuma wanda ya qulla wannan sharri wato Abdullahi bn Ubayy bn Salul (shugaban munafuqai) a kan waxannan abokai na Annabi (SAW), sai Allah Ya ce a kansa: “Kuma wanda ya jivinci girmansa (qazafin) daga gare su, yana da azaba mai girma.” (Q:24:11).
Domin duk wanda aka ce mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko matarsa ko xansa mutanen banza ne, to kai-tsaye shi aka wulaqanta.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan wanda kuka amince da addininsa da halayensa ya zo neman aure a wurinku ku ba shi. Idan ba ku yi haka ba, fitina da fasadi za su watsu a bayan qasa.” Muslim da Ibn Majan suka ruwaito.
Xaukar ’ya mace ku ba namiji yana nufin kun haxa aboki da abokiya ne, dole ne ku lura da irin mutumin da za ku haxa ’yarku da shi. Saboda ko ya zame mata aboki nagari ko na sharri. Domin haka ne Annabi (SAW) ya bayar da siffofin miji nagari, wato shi ne mai addini da halaye masu kyau. Idan ba ku kula da haka ba, varna za ta yi yawa a bayan qasa. Annabi (SAW) ya sake cewa: “Kada ka yi aboki said a mumini, kada ka ciyar da abincinka sai ga mai tsoron Allah…” Tirmizi ya ruwaito. A wani Hadisin kuma Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira kada ya zauna a kan teburin giya.” Tirmizi.
Mugun aboki shi ne babban maqiyi ranar qiyama, kamar yadda Allah Ya nuna cikin faxinSa: “Kuma waxanda suka kafirta suka ce: “Ya Ubangijinmu! Ka nuna mana waxannan biyun da suka vatar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a qarqashin qafafunmu, domin su kasance daga qasqantattu.” (Q:41:29). Sannan Ya ce: “Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, za Mu lulluve shi da Shaixan ya zama abokinsa. Kuma lallai su (shaixanu) haqiqa suna kange su daga hanya, kuma suna zaton su masu shiryuwa ne. Har a lokacin da (abokin Shaixan) ya zo Mana (ya mutu), sai ya ce: “Da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum.” (Q:43:36-38). Kuma Ya sake cewa: “Masoya a yinin nan, sashinsu zuwa ga sashi maqiya ne, face masu taqawa (su kam masu son juna ne)” (Q: 43: 67). Kuma Ya ce: “Kuma waxannan da suka yi xa’a ga Allah da ManzonSa, to, waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi ni’ima a kansu, daga annabawa da masu yawan gaskatawa da masu shahada da salihai. Kuma waxannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya.” (Q: 4: 69).
Ya zo a cikin Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a qarqashin inuwar Al’arshi a ranar da babu wata inuwa sai ita.” Daga cikinisu akwai: “Mutane biyu da suka so juna (suka yi abota) saboda Allah a kan haka suka haxu, kuma a kan haka suka rabu.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Ma’ana abotansu ya zamo aikin Allah ne yake haxa su, kuma shi yake raba su, ba aikin Shaixan ba.
Allah Ya xaukaka Musulunci da Musulmi, kuma Ya qasqantar da kafirci da kafirai, amin.
Daga hudubar Malam Abdulmumin A. Khalid, Masallacin Badar, Kubwa- Abuja
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman tsarinsa daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta mawa sai Allah. Kuma ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.
Bayan haka, ya ku bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah, ku san irin mutane da za ku yi abota da su. Kuma ku lura da irin wadanda ’ya’yanku ke abota da su. Abokai suna da tasiri kwarai game da mutuncin mutum. Idan abokan mutum ba mutanen kirki ba ne, babu wanda zai yarda cewa shi muutumin kirki ne. Ku dubi yadda Alkur’ani ya bayyana mutuncin abokan (Sahabban) Annabi (SAW), kuma ya dauki matakai masu tsanani kan duk wanda yake neman y ace sub a mutanen kirki ba ne. Saboda hakan zai iya shafar Annabi (SAW). Sai Allah Ya ce: (Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai masu rahama ne a tsakaninsu. kana ganin su suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu da yardarSa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu daga kufan sujuda. Wannan shi ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma a cikin Linjila ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya karfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan kafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) Ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa’adi ga wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai daga cikinsu da gafara da ijara mai girma.” (k:48:29).
Kuma lokacin da munafukai suka yi ta zargin sahabinsa Safwan bn Mu’addil da Uwar Muminai A’isha (RA) da aikata fasikanci, sai Allah Ya saukar da ayoyin Alkur’ani domin kare su da kuma ladabtar da wadanda suka yi ta yada maganar. Shi kuma jagoran kulla wannan makirci, Allah Ya yi alkawarin sai Ya yi masa azaba. Sai Allah Ya ce: “Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma mmiyagun maza domi miyagun mata suke, kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke, kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. Wadancan su ne wadanda ake barrantawa daga abin da (masu kazafi) suke fada, kuma suna da gafara da arziki na karimci.” (k:24:26).
Kuma an ladabtar da wadanda suka wannan kazafi kamar haka: “A lokacin da kuke marabarsa da harsunanku kuma kuna cewa da bakunanku abin da ba ku da wani ilimi game da shi, kuma kuna zaton sa mai sauki, alhali kuwa a wurin Allah, babba ne. Kuma don me a lokacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, “Ba ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan kiren karya ne mai girma. Allah Yana yi muku wa’azi kada ku koma ga irinsa har abada, idan kun kasance muminai.” (k:24:15-17).
Shi kuma wanda ya kulla wannan sharri wato Abdullahi bn Ubayy bn Salul (shugaban munafukai) a kan wadannan abokai na Annabi (SAW), sai Allah Ya ce a kansa: “Kuma wanda ya jibinci girmansa (kazafin) daga gare su, yana da azaba mai girma.” (k:24:11).
Domin duk wanda aka ce mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko matarsa ko dansa mutanen banza ne, to kai-tsaye shi aka wulakanta.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan wanda kuka amince da addininsa da halayensa ya zo neman aure a wurinku ku ba shi. Idan ba ku yi haka ba, fitina da fasadi za su watsu a bayan kasa.” Muslim da Ibn Majan suka ruwaito.
daukar ’ya mace ku ba namiji yana nufin kun hada aboki da abokiya ne, dole ne ku lura da irin mutumin da za ku hada ’yarku da shi. Saboda ko ya zame mata aboki nagari ko na sharri. Domin haka ne Annabi (SAW) ya bayar da siffofin miji nagari, wato shi ne mai addini da halaye masu kyau. Idan ba ku kula da haka ba, barna za ta yi yawa a bayan kasa. Annabi (SAW) ya sake cewa: “Kada ka yi aboki said a mumini, kada ka ciyar da abincinka sai ga mai tsoron Allah…” Tirmizi ya ruwaito. A wani Hadisin kuma Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira kada ya zauna a kan teburin giya.” Tirmizi.
Mugun aboki shi ne babban makiyi ranar kiyama, kamar yadda Allah Ya nuna cikin fadinSa: “Kuma wadanda suka kafirta suka ce: “Ya Ubangijinmu! Ka nuna mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a karkashin kafafunmu, domin su kasance daga kaskantattu.” (k:41:29). Sannan Ya ce: “Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, za Mu lullube shi da Shaidan ya zama abokinsa. Kuma lallai su (shaidanu) hakika suna kange su daga hanya, kuma suna zaton su masu shiryuwa ne. Har a lokacin da (abokin Shaidan) ya zo Mana (ya mutu), sai ya ce: “Da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum.” (k:43:36-38). Kuma Ya sake cewa: “Masoya a yinin nan, sashinsu zuwa ga sashi makiya ne, face masu takawa (su kam masu son juna ne)” (k: 43: 67). Kuma Ya ce: “Kuma wadannan da suka yi da’a ga Allah da ManzonSa, to, wadannan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni’ima a kansu, daga annabawa da masu yawan gaskatawa da masu shahada da salihai. Kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya.” (k: 4: 69).
Ya zo a cikin Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a karkashin inuwar Al’arshi a ranar da babu wata inuwa sai ita.” Daga cikinisu akwai: “Mutane biyu da suka so juna (suka yi abota) saboda Allah a kan haka suka hadu, kuma a kan haka suka rabu.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Ma’ana abotansu ya zamo aikin Allah ne yake hada su, kuma shi yake raba su, ba aikin Shaidan ba.
Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi, kuma Ya kaskantar da kafirci da kafirai, amin.