Shahararren dan kwallon Ingila Dabid Beckham ya kusa mallakar sabon kulob a gasar rukuni-rukunin Amurka da ake wa lakabi da Major League Soccer, (MLS).
Ana sa ran idan ya sayi kulob din zai ajiye shi ne a garin Miami da ke kasar kamar yadda tsohon dan kwallon ya nuna sha’awarsa a kan haka.
Rahoton da kafar sadarwar naij.com ta kalato ya nuna tuni Beckham ya fara yunkurin ginawa sabon kulob din filin wasa irin na zamani na kashin kansa a birnin Miami don ganin ya zauna da gindinsa.
A ranar Talatar da ta wuce ne Beckham tare da wasu daga cikin shugabannin rukunin kamfanoninsa da ke Amurka da kuma Kwamishinan kula da gasar rukunin Amurka (MLS) mai suna Don Garber suka ziyarci Miami don tattauna batun da hukumomin da abin ya shafa.
Tun a shekarar 2007 jim kadan da komawarsa kulob din Los Angeles Galady Dabid Beckham ya fara yunkurin mallakar kulob na kashin kansa bayan kwantaragin da ya sanya hannu a kai ya amince masa da yin haka. Yarejejeniyar ta ce dan kwallon zai iya mallakar wani kulob a gasar rukunin Amurka idan ya so yin haka wanda kudinsa bai gaza Dala miliyan 25 kwatankwacin Naira biliyan 4 da miliyan 150 ba idan ya yi ritaya da kwallo. Kuma ana jin wannan ne ya ja ra’ayinsa ya koma Amurka don cigaba da buga kwallo.
Don haka yanzu da maganar ta taso ake ganin tsohon dan kwallon ba zai samu matsala wajen mallakar kulob a Amurka ba.
Sai dai ya zuwa wannan lokaci ba a ambaci takamaiman kulob din da tsohon dan kwallon zai mallaka ba. Sannan akwai yiwuwar Beckham ya fafata a cinikin tare da wasu shahararrun masu kudi, daya dan kasar Bolibia mai suna Marcelo Claure da kuma dan Birtaniya Simon Fuller. Haka kuma ba a ambaci rana da shekarar da ake tunanin kulob din zai fara yin wasa ba.
Dabid Beckham ya fara yunkurin sayen wani kulob a Amurka
Shahararren dan kwallon Ingila Dabid Beckham ya kusa mallakar sabon kulob a gasar rukuni-rukunin Amurka da ake wa lakabi da Major League Soccer, (MLS).Ana sa…
