Wata dabi’a da aka jarrabi mutane da yawa da ita a wannan zamani, maza da mata, manya da yara, ita ce ta zuwa wajen matsafa, bokaye, ’yan duba da ’yan tsubbu, don neman taimako a wajensu, domin sanin abin da zai zo nan gaba ko kuma neman wata biyan bukata.
Wannan ba karamar halaka ba ce mai tabarwa duniya da lahira.
- Hanyoyin Nishadantar da iyali bayan Ramadan
- Mazauna sun firgita da ganin makwabci a cikin ’yan bindigar da suka kai musu hari
Mafi akasari mu mata mu ne muka fi afkawa cikin wannan mummunar dabi’a, musamman ’yan matan da suke fafutukar neman mazajen aure ido rufe, kamar yadda bincike ya nuna ko kuma matan aure da ke da kishiyoyi ko ake shirin yi musu.
Wannan mummunar dabi’ar ta hallakar ko kuma tana kan hallakar da kaso mai tarin yawa na mata a wannan zamani. Raba Miji da Matarsa; Wannan dabi’a ta zama ruwan dare a tsakakkanin ‘Yan mata da Matan aure.
Sai kaga budurwa da taimakon iyayenta sun himmatu wajen kai kawo gurin bokaye da malaman tsubbu duk don suga yarsu ta auri wani saurayi da ake kwadayin abinda ke tattare dashi.
Suma a nasu bangaren, Matan da ke gidan mazajen su kokarin ganin suke sun mallake mijin da suke tare dashi, ko kuma kishiyar da suke zaune da ita domin tabbatar da komai suka bada umarni haka za’a aiwatar dashi, ba tare da musu ko jayayya ba.
A wasu lokutan ma wannan ba iya ita ce bukatar su ba harma da ganin sun kori kishiyar da suke zaune da ita, ko kuma ganin sun raba mijin da ‘yan uwa da abokan arziki, kai a wani lokutan ma ita kanta rayuwar suke kokarin tsaidawa.
Ana samun mata masu yawa da dabi’ar bin ‘yan tsibbu da Bokaye saboda manufofi daban daban.
Me ke kai mata ga wannan dabi’ar?
Mafi yawan mata abinda yake kai su wajen bokaye dalilai ne kamar haka:
1. Jayayya da umurnin Allah 2. Fada da kaddarar Allah 3. Sabawa umurnin manzon Allah 4. Rashin imani 5. Rashin tausayi 6. Hassada 7. Rashin tawakkali
Manyan haduran bin bokaye
Daga cikin manyan hadurran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai:
1. Shirka ga Allah: Wannan da’ar da kuma cika sharuddan da aljanun da bokayen ke aiki da, shi ne bakar shirka. Domin bautawa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga wanin Sa, kamar yanka dabba domin wanin Sa, ko kuma cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba.
2. Rashin Dogaro ga Allah: Mai sihiri ko kuma mai neman a yi masa sihirin bai yarda da cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma shi ne mai taimakonsa ba, kuma shi kadai ne mai iya fitar da shi daga kowacce matsala, ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa.
3. Cutar da Mutane: Wannan kuma babban abu ne da ya shafi hakkin shi wanda aka cutar din, domin har abada Allah zai bi ki da alhakinsa har sai in ya yafe miki, bayan babban laifin shirkar da aka yi.
4. Yada Firgici da Waswasi: idan sihiri ya yadu tsakanin al’umma, to komai kankantar abin da ya faru ga mutum ko wani nasa sai ya fara zaton cewa sihiri wani ya yi masa, tun bai yi bincike ko ya je wurin likita ya rasa magani ba. Wannan kan yawan faruwa a wannan lokaci da muke ciki.
5. Janyo Fushin Allah Madaukaki: Duk al’ummar da ta fada cikin wannan mummunan hali kuma malamanta suka yi shiru ba su fadakar da mutane kan hadarinsa ba, to fushin Allah zai iya fada mata kuma ta rasa albarka, ta rasa zaman lafiya, kamar dai halin da kasar mu take a ciki yanzu.
Rubutawa: Samira Bello Shinko [email protected]