✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun magance MMM

Assalamu alaikum, barkan da sake haduwarmu cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta (MMM), watau na fitar maniyyi…

Assalamu alaikum, barkan da sake haduwarmu cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta (MMM), watau na fitar maniyyi da wuri. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin. A yau za mu duba dabarun da maigida zai yi amfani da su don ya gwanance wajen iya jan ragamar sha’awarsa. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dabara ta 1: Kegel
Kegel shi ne samfurin motsa jiki (edercise) musamman don karfafa jijiyoyin al’aura. wani Ba’amurken likita mai suna Arnold Kegel ne ya yi gam-da-katar din samar da wannan samfurin motsa jikin jijiyoyin al’aura shekaru sama da sittin da suka wuce, musamman don karfafa jijiyoyin ’yammatanci bayan haihuwa. Daga baya binciken masana kimiyya ya tabbatar Kegel yana amfani ga kara lafiyar sha’awar ba mata kadai ba har maza, kuma musamman yana warkar da matsalar fitar maniyyi da wuri da ta raunin mazakuta matukar za a nace ana yinsa kamar ibada, watau ba fashi.
Hanya mai sauki ta gane wadannan jijiyoyi da fahimtar yadda za a motsa su ita ce, da an fara fitar da fitsari, kafin ya gama fita sai a tsayar da shi, to wadannan jijiyoyi su ne masu tsayar da fitsari in ana cikin yinsa, in aka fahimci haka, a hankali sai a rinka motsa su ko da ba lokacin fitsari ba, sai a rika yunkurin sake da dakatar da zubar fitsari ba tare da lallai wai ana fitsarin ba. Da farko sai a fara; a yi yau, gobe a huta sannan jibi a yi, gata a huta, har sai an lakanci abin sosai sannan ne za a rika yi kullum. Da farkon farawa, da wuya ne a iya rikewa  fiye da dakika 5, amma in aka saba, aka kware, wata rana sai a ga ana rikewa har minti biyar ko abin da ya yi sama. Don haka sai ana yi ana kara tsawon lokacin yin, tun ana yi na tsawon minti daya sau uku kullum, sai a rika karawa har zuwa iya lokacin da aka ji ya yi daidai. Indai har aka dage da wannan, cikin sati biyu zuwa uku za a fara ganin irin canjin da ake so insha Allah. Kegel ya amfani mutane da yawa maza da mata wajen warkar masu da matsalolin sha’awarsu, amma fa dole sai an nace, an dage kuma an yi hakuri. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Dabara ta 2: Hora sha’awa
Kamar yadda na yi bayani a baya, iya jan ragamar sha’awa shi ne babban maganin matsalar fitar maniyyi da wuri. Ana iya hora sha’awa ta hanyar wani dan kwas na ‘yi da dakatawa’ wanda ke horas da ma’aikatar hankalin mai fama da wannan matsalar ya lakanci yadda zai rika jan ragamar sha’awarsa har ya kwato ‘yancinsa daga sha’awarsa ya kasance ta dawo karkashin ikonsa, sai yadda ya yi da ita, domin wannan ce hanya daya da tafi duk sauran tabbas wajen tafiyar da wannan matsalar.
Sai magidanci ya rika horar da kansa sau uku a kullum tare da taimakon uwargidansa, a yi ta yi ba fashi na tsawon wata uku, don ya lakanci yadda zai rika sarrafa sha’awarsa. Yadda ake wannan horo shi ne: sai a hauhawar da sha’awar har sai ta kai lokacin da take gab da kubcewa, sai a tsayar da ita nan take, kamar ta hanyar daina motsi, da karkatar da tunanin ma’aikatar hankali zuwa ga wani abu daban, ko mutum ya rika tuna wani abu da kwata-kwata bai da nasaba da ibadar aure, kamar a tuna wurin aiki, ko a hararo tulin bola, ko dai duk wani abu da zai dauke hankalin mutum na dan wani lokaci har sha’awar ta dan sauka sannan a ci gaba, a yi wannan ‘yi da dakatawar’ sau uku a kowace rana. In aka nace da yin wannan horon, cikin wata daya za a fara ganin canji cikin yardar Allah SWT.
Dabara ta 3: Ja da ajiye dogon numfashi
Fitar numfashi da sauri-da-sauri lokacin gabatarwar ibadar aure na hayayyako da sha’awa, hakan kuma ke haifar da fitar maniyyi da wuri. Jan dogon numfashi da sakewa kadan-kadan kuma a hankali na rage karfin gudun sha’awa, ta yadda za ta tafi a hankali kuma daidai da lokaci, wannan zai rage saurin fitar maniyyi da wuri. Sannan ja da ajiye dogon numfashi na tafiyar da fargaba da duk wani jin dar-dar da mutum ke ji a lokacin gabatarwar ibadar aure.
Zan dakata a nan, sati na gaba sauran bayani na zuwa Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa kodayaushe, amin.Assalamu alaikum, barkan da sake haduwarmu cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta (MMM), watau na fitar maniyyi da wuri. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin. A yau za mu duba dabarun da maigida zai yi amfani da su don ya gwanance wajen iya jan ragamar sha’awarsa. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dabara ta 1: Kegel
Kegel shi ne samfurin motsa jiki (edercise) musamman don karfafa jijiyoyin al’aura. wani Ba’amurken likita mai suna Arnold Kegel ne ya yi gam-da-katar din samar da wannan samfurin motsa jikin jijiyoyin al’aura shekaru sama da sittin da suka wuce, musamman don karfafa jijiyoyin ’yammatanci bayan haihuwa. Daga baya binciken masana kimiyya ya tabbatar Kegel yana amfani ga kara lafiyar sha’awar ba mata kadai ba har maza, kuma musamman yana warkar da matsalar fitar maniyyi da wuri da ta raunin mazakuta matukar za a nace ana yinsa kamar ibada, watau ba fashi.
Hanya mai sauki ta gane wadannan jijiyoyi da fahimtar yadda za a motsa su ita ce, da an fara fitar da fitsari, kafin ya gama fita sai a tsayar da shi, to wadannan jijiyoyi su ne masu tsayar da fitsari in ana cikin yinsa, in aka fahimci haka, a hankali sai a rinka motsa su ko da ba lokacin fitsari ba, sai a rika yunkurin sake da dakatar da zubar fitsari ba tare da lallai wai ana fitsarin ba. Da farko sai a fara; a yi yau, gobe a huta sannan jibi a yi, gata a huta, har sai an lakanci abin sosai sannan ne za a rika yi kullum. Da farkon farawa, da wuya ne a iya rikewa  fiye da dakika 5, amma in aka saba, aka kware, wata rana sai a ga ana rikewa har minti biyar ko abin da ya yi sama. Don haka sai ana yi ana kara tsawon lokacin yin, tun ana yi na tsawon minti daya sau uku kullum, sai a rika karawa har zuwa iya lokacin da aka ji ya yi daidai. Indai har aka dage da wannan, cikin sati biyu zuwa uku za a fara ganin irin canjin da ake so insha Allah. Kegel ya amfani mutane da yawa maza da mata wajen warkar masu da matsalolin sha’awarsu, amma fa dole sai an nace, an dage kuma an yi hakuri. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Dabara ta 2: Hora sha’awa
Kamar yadda na yi bayani a baya, iya jan ragamar sha’awa shi ne babban maganin matsalar fitar maniyyi da wuri. Ana iya hora sha’awa ta hanyar wani dan kwas na ‘yi da dakatawa’ wanda ke horas da ma’aikatar hankalin mai fama da wannan matsalar ya lakanci yadda zai rika jan ragamar sha’awarsa har ya kwato ‘yancinsa daga sha’awarsa ya kasance ta dawo karkashin ikonsa, sai yadda ya yi da ita, domin wannan ce hanya daya da tafi duk sauran tabbas wajen tafiyar da wannan matsalar.
Sai magidanci ya rika horar da kansa sau uku a kullum tare da taimakon uwargidansa, a yi ta yi ba fashi na tsawon wata uku, don ya lakanci yadda zai rika sarrafa sha’awarsa. Yadda ake wannan horo shi ne: sai a hauhawar da sha’awar har sai ta kai lokacin da take gab da kubcewa, sai a tsayar da ita nan take, kamar ta hanyar daina motsi, da karkatar da tunanin ma’aikatar hankali zuwa ga wani abu daban, ko mutum ya rika tuna wani abu da kwata-kwata bai da nasaba da ibadar aure, kamar a tuna wurin aiki, ko a hararo tulin bola, ko dai duk wani abu da zai dauke hankalin mutum na dan wani lokaci har sha’awar ta dan sauka sannan a ci gaba, a yi wannan ‘yi da dakatawar’ sau uku a kowace rana. In aka nace da yin wannan horon, cikin wata daya za a fara ganin canji cikin yardar Allah SWT.
Dabara ta 3: Ja da ajiye dogon numfashi
Fitar numfashi da sauri-da-sauri lokacin gabatarwar ibadar aure na hayayyako da sha’awa, hakan kuma ke haifar da fitar maniyyi da wuri. Jan dogon numfashi da sakewa kadan-kadan kuma a hankali na rage karfin gudun sha’awa, ta yadda za ta tafi a hankali kuma daidai da lokaci, wannan zai rage saurin fitar maniyyi da wuri. Sannan ja da ajiye dogon numfashi na tafiyar da fargaba da duk wani jin dar-dar da mutum ke ji a lokacin gabatarwar ibadar aure.
Zan dakata a nan, sati na gaba sauran bayani na zuwa Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa kodayaushe, amin.