Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa da shi da Sule Lamido har yanzu suna kan kujerar mulki, da sun fito ƙarara sun ƙalubalanci Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Amaechi ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna ‘Being True to Myself’ da aka gudanar a Abuja.
- Ko yanzu aka yi zaɓe Tinubu ne zai yi nasara — Oshiomhole
- DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya
“Da mun fito da ƙarfinmu, mun ƙalubalanci gwamnati, mun kalubalanci shugaban ƙasa,” in ji Amaechi.
“Haka muka saba a lokacin muna Gwamnoni. Muna da kishin ƙasa da ƙwarin gwiwar sauya al’amura.”
Ya bayyana yadda dangantakar siyasar da ke tsakaninsa da Lamido, inda ya ce duk da kasancewar suna da alaƙa a wancan lokaci, sun raba gari ne lokacin da Lamido ya ƙi komawa jam’iyyar APC domin su haɗa ƙarfi wajen kayar da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
“A lokacin, Lamido ya zaɓi kafa sabuwar jam’iyya – SDP, amma mu mun yarda cewa za mu fi samun nasara a jam’iyyar APC,” in ji Amaechi.
“Wannan ne ya sa hanyoyinmu suka rabu.”
Shugaba Tinubu, wanda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya wakilta a taron, ya ce shugaban ƙasa ya amince da mahawara mai ma’ana, amma hakan ba zai hana shi yi wa ƙasar nan abin da ya dace ba.
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ma ya yi jawabi a wajen taron, inda ya bayyana Lamido a matsayin jagoran da ke da gaskiya da tsayawa kan aƙidarsa, inda ya ce lokacin da Lamido ke Ministan Harkokin Waje, ya taimaka wajen dawo da mutuncin Najeriya a idon duniya.
Obasanjo ya ce, “Sule ya taɓa faɗa, ‘Idan ka ga ban cancanta ba, ka ba ni minti biyar kawai na yi murabus. Amma ka da ka tambaye ni takardar murabus da ba ta da kwanan wata.’ Na girmama wannan matsayi nasa.”
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya wakilci Janar Abdulsalami Abubakar, ya jinjina wa littafin Lamido da cewa ya bayyana tarihin siyasar Najeriya da darusan da matasa za su amfana da su.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Iyorchia Ayu, wanda ya yi nazari a kan littafin, ya soki gwamnatin APC da cewa ta zama annoba ga Najeriya.
Ya buƙaci Lamido da ya ci gaba da rubuta littattafai domin su zama jagora ga ’yan Najeriya.