Salisu Umar dan shekara 26 mai jigilar amfanin gona a Dei-dei da ke Abuja. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya sayi mota da kudin kwadagon da yake samu a gona, ya kuma yi bayanin yadda ya dogara da kansa ta hanyar noma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka
Salisu: Sunana Salisu Umar, shekara ta 26, daga karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano nake, na dawo Abuja kimanin shekara 15 da ta gabata.
Aminiya: Yaya ka fara jigilar amfanin gona?
Salisu: Bayan na dawo Abuja ne sai na fara jigilar amfanin gona, kodayake daga farko kwadago nake yi, inda zan yi noma a sallame ni kowace rana. A rana akan biya ni Naira 350 ko fiye da haka.
Aminiya: A yanzu kana da motar da kake amfani da ita wajen jigilar amfanin gona, ta yaya ka tara kudin da ka sayi mota?
Salisu: Na tara kudin da na sayi motata bolkswagen Golf ne ta hanyar ajiye wani abu daga kudin kwadago da ake biya na, idan me gona ya sanya ku aiki, to zai samar muku da abincin da za ku ci, don haka ba ni da matsalar sayan abinci kowace ranar da nake aiki, na tara kudin ne bayan shekaru masu yawa da na dauka ina ajiyewa. Na tara kudin da ya kai har na sayi mota.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka koma jigilar amfanin gona maimakon ci gaba da kwadago?
Salisu: Daga lokacin da na tara kudin da zan iya sayan mota, sai na yanke shawarar in saya don in fara jigila da ita, wanda hakan yana nufin na samu ci gaba ke nan, hakan ya sanya na ce tun da na san harkar noma, kuma na saba da manoma, to me zai hana in rika yi musu jigilar amfanin gonarsu zuwa kasuwanni su rika biya na. Cikin ikon Allah bayan na sanar da su sai suka amince, da ma na fada muku na san manoma da yawa, sai suka rika kira na ina yi musu jigilar amfanin gonarsu zuwa kasuwanni. Nakan fada musu kudin da za su biya ni bayan na yi la’akari da yawan kayansu ko kuma nisan wurin da zan kai musu.
Aminiya: Kamar nawa kakan samu duk rana?
Salisu: Ya danganta da nisan wuri da kuma yawan je-ka-ka-dawo a rana, wata rana nakan samu Naira 19,000, wata rana kuma nakan samu 3000. Da kudin da nake samu ne nake daukar nauyin ’ya’yana 3. Dukkansu suna makaranta, ba na bata lokaci wajen biya musu kudin makaranta.
Aminiya: Wadanne matsalaloli ka fuskanta yayin jigilar amfanin gona?
Salisu: Ku taimaka ku fada wa gwamnati cewa yawancin hanyoyin kauyukan Abuja ba su da kyawu, na kashe kudi mai yawa wajen gyaran motata, kuma takan lalace ne sakamakon rashin kyawun hanya.
Aminiya: Wanne aiki kuma kake yi wa manoma?
Salisu: Nakan kasance kamar dillali da ke taimaka wa manoma da masu saya don a cim ma matsaya, nakan taimaka wa manoma yadda za su yi ciniki da kwastomominsu, abin da ya sa nake jin dadi shi ne, manoma da kwastominsu duka sun yarda da ni, nakan samu kamisho idan cinikin da na shiga ya kammala.
Aminiya: Kamar wadanne amfanin gona kake dillanci?
Salisu: Nakan yi dillancin kayan lambu kamar tumatir da attarugu da albasa da ganyayyaki. Akan sayar da kwandon tumatir daga Naira 7,000 zuwa 9,000, kwandon attarugu kuma daga 17,000 zuwa 18,000. Nakan kai su kasuwar Dei-Dei da sauran kasuwanni. Wadansu kuma nakan yi jigilarsu daga Katsina da Kano don a sayar da su a Dei-Dei. Idan ma ba zan samu lokacin yi musu jigila ba, nakan hada su da wadansu direbobi da za su kawo musu kayansu cikin kwanciyar hankali.