Shin ka taɓa tunanin yaya masu sana’ar yankar farce suke gudanar da ita shekara 50 da suka gabata a Najeriya A ganinka nawa ake biyan kuɗin gyaran farce a wancan lokaci, kuma yaya yanayin cinikin masu yin ta? Nawa kake ganin mai sana’ar zai iya tarawa a yini? A gininka a tsawon wane lokaci mai sana’ar yankan farce na gargajiya zai iya tara kuɗi ya gina gida ko ya biya kuɗin kujerar aikin Hajji?
Malam Salihu Abdullahi wani dattijo ne mai shakara kimanin 65, wanda ya shafe sama da shekara 50 yana sana’ar yankan farce a Kano, kuma har yanzu bai daina ba.
A zantawarsa da wakilinmu, dattijo ya ba mu labarin yadda sana’ar take a lokacin daya shige ta shekara 50 da suka gabata da barazanar da ya fuskanta a hannun dakarun soji a bakin aikinsa, yana mai cewa duk inda ya je a duniya, sai ya yi wannan sana’a ko da a kan jariri sabon haihuwa ne.
Kobo ɗaya ake biya kuɗin aiki:
Alhaji Salihu, wanda muka same shi a zaune a ƙofar gidansa da ke a unguwar Ɗandinshen Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano, ya ce ya faro sana’ar tun ana biyan sa Kobo ɗaya.
- Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero
- Yadda ’yan ta’adda suka kashe masu gaisuwar ta’aziyya 30 a Katsina
Idan aka kwatanta kuɗin yankan farce da ake biyan Alhaji Abdullahi a wancan lokaci da kuɗin aikin a yanzu, sai an ninka kuɗin da ake biyan sa a wancan lokaci sau dubu ɗari biyu, kafin a ya kai Naira 200 da ake biya kuɗin gyaran farce a yanzu.
“Na faro wannan sana’a lokacin Fam daya. Ana ba ni Kobo ɗaya, kobo biyu, har ya zama taro (Kobo huɗu) har ta kai Sisi (Kobo biyar), Sule (Kobo goma, zuwa Sule biyu (Kobo ashirin), har kawo yanzu (Naira 200),” da nake ci gaba da wannan sana’ar in ji Alhaji Salihu.
Na biya kujerar Hajji na gina gida:
Ya bayyana wa Aminiya cewa daga ’yan kwabban da yake samu a sana’ar ya tara kuɗi ya sayi fili ya gina gidan kansa, ya kuma biya wa kansa kujerar aikin Hajji.
“Ta dalilinta (ita wannan sana’a) Allah Ya sa na samu ikon tafiya je aikin Hajji sauke farali. Bayan na sauke farali kuma na ci gaba ginina, dama da ita na tara kuɗin sayen filin kafin in je Makkah. Na yi shekaru da sayen filin dama, kuma na fara ginin kafin in je Makkah,” kamar yadda ya shaida mana.
Dattijon ya ce a lokacin da ya je sauke farali a Ƙasa Mai Tsarki ma sai da ya ci gaba da gudanar da sana’ar. Don haka, “Da Allah Ya sa na ke na dawo na samo wannan kuɗi na leburanci, sai na zo ma ci gaba da ginin, har Allah Ya ba ni iko na rufa, har ga shi ina da shekara 15 da tarewa a ciki.”
Da muka nemi jin shekarar da ya je aikin Hajji da kuma kuɗin jera a lokacin, sai Alhaji ya ce, “ba na riƙe kuɗin ba, amma dai lokacin [Malam Ibrahim Shekarau ne Gwamnan Kano].
“Ba zan iya tantance kudin kujerar a lokacin ba, saboda Ni dai rubuta rasit aka yi, aka karɓi fasfo ɗina aka yo min biza. Kamfani ya yi min biza aka ba ni kuɗin guzurina. Na bar wa iyalai abin da za su ci abinci, na sa sauran dalolina na tafi da su ni ma, kuɗin guzurina.”
Idan za a iya tunawa. Malam Ibrahim Shekarau ya yi gwamnan Kano ne daga shekarar 2003 zuwa 2011.
Sana’ar yankan farce a Saudiyya:
Ya ce, “Da ana cewa ana hana tafiya da aska idan wanzami ne, da almakashi, sai na ba wani jami’in tsaro na FAAN (Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama) daga filin jirgi, na ba shi, almakusana na ce ya kai min gida. Ɗan unguwarmu ne, lokacin ina Rijiyar Lemo.”
Bayan sun kammala aikin Hajji, suka dawo masauki daga wurin Jifa sai Alhaji Salihu ya nemi inda zai sayi almakusa ya fara sana’arsa, idan wani wanda suke tare da shi, “ya raka ni Dogon Gida muka je na sayi almakusa guda biyu, dama na tafi da omo da mai da ɗan dutse na wasawa.
Ƙarafunan su ne ake cewa kwamfuta za ta nuna za a qwace, su ne na ɗaure na bayar aka kawo min gida.
“Da na je can na sayi gida biyu da haɗa waɗannan kaya, su nake aiki da su har muka tashi tasowa. Idan muka yi aikin kwana muka taso muka ka yi barci, zan ci gaba da yi wa abokan aikina.”
Ya bayyana man cewa ya haɗa yankan farce da aikin lodi a Saudiyya, inda bayan sun kammala aikin lodi a cikin dare, idan yari ya waye yakan ci gaba da sana’arsa har zuwa Magariba.
Ya ce, “A cikin filin jirgi ma da muka zo za mu dawo Nijeriya, bayan mun gama wannan lodi, kan yin [yankan farce] kullum har zuwa maraice.
“Duk abin da zan ci a nan ban taɓa guzurina ba. Abin da na yi yankan farce da shi zan ci abinci a ranar. Har ma daga ciki na samu kuɗin da na sayi wata tsaraba wadda taho gida da ita.”
Alhaji Salihu ya ce tunda har ya yi wannan sana’a a Saudiyya, to babu inda ba zai yi ta ba, “duk inda na ne zan yi, zan tafi da su (almakusan). Tunda ma na yi a Makkah, balantana wani wuri. Kowane gari za yanzu fa su zan tafi, saboda duk inda ta faɗi sha, a dai samu a ci abinci.”
Ya ce ko da matsala ya samu a matsayin matafiyi, sana’arsa zai yi, “in samu kuɗin mota ko guzuri.” Ya ce ba ya tunanin daina sana’ar saboda ya samu wani ci-gaba babba.
“Sai dai idan wani aikin ya samu gwamnati ne sai dai in goya biyu. Idan na yi wancan na tashi, to kuma na zo na yi sana’ata
wadda nake yi tun ina ƙanƙani.”
Kwalliya ta biyu kuɗin sabulu:
Da yake shaida mana yadda sana’ar ta yi masa rana, sai ya kada baki ya ce, “Da ita wannan sana’a na wayi gari tun yarinta, ina yin ta ina kuma samun rufin asiri, na tara abin da ma sayi fili, na kuma sayar da filin na zo nan na sayi wani fili, ga shi yanzu ina ƙofar gidan da nake kwana.
“Duk kuma da wannan sana’a na mallaki waɗannan abubuwan: keken da nake hawa da iyalaina guda biyu duk da ita na yi. Sannan da yarana da na aurar guda uku, ga ta huɗu da za a yi nan gaba,” in ji shi a tattaunawarmu da shi.
Yadda na koyi sana’ar:
Ya shaida mana cewa ya koyi sana’ar tun yana yana ɗan shekara 10 duniya, ya ci gaba da cewa, “yayana ya koya min ita kuma na ga ina samu, kuma na tsaya a kanta.
A wancan lokacin idan ka je kasuwa ka yi yankan farce, abin da za Ka kashe ka ci abinci bai wuce kwabbai uku zuwa Kobo huɗu ba.
Sauran abin da ka samu za ka tafi gida da abinka. Kuma lokacin ban isa aure ba, ba wani nauyi nake da shi a gida ba.”
Saboda da maza jari:
Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa a sakamakon daɗewarsa a sana’ar ya kasance mai gyaran farcen tsohon Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi da wasu manyan attajirai da ’yan siyasa da malaman addini.
“Sule Jikan Korau na Katsina sai Alhaji Ibrahim Babankowa wanda ya yi Kwamishinan ’Yan Sanda amma ya rasu, sai Rimi Allah Ya jiƙan shi, sai Sabi’u Baƙo shi ma za a sa shi cikin masu kuɗaɗe, sai Nasiru Ahali. Sannan na yi wa wani mutumin Sardauna ana ce masa Alhaji Suke Ojali.”
“Lokacin da nake Birget an taɓa kira na na yi wa yaro gyaran farce na a yi sunansa ba. Nan wajen Gama Hotel, aka ɗauki mini shi a tsumma aka ce in yanke masa farce. Ko yanzu ka kawo min jariri da bai yi kwana bakwai ba zan yi masa yankan farce.”
“In ka tuna baya na gaya maka a baya cewa ga Kwamanda na soja da inifom da komai da yaransa a ofis, ya gaya min cewa in na yanke shi zai kulle ni, amma gabana bai faɗi ba, ban kuma ayyana yankan zai faru ba, kuma bai faru ba. Kuma har ya zama an dauƙe shi daga iyafot ya zama ni ke masa yankan farce kuma ban taɓa taɓa shi ba, har aka ɗauke shi daga Nijeriya.
“Ba wai alfahari ba ko ina yabon kaina ba, in dai maganar yankan farce ne, a yanzu ko a gobe, ko shugaban ƙasa na ina ne, ba na Nijeriya ba, aka kira ni zan iya yi masa hankali kwance, ba tare da wani shakku ko ina ɗar-ɗar ba.”
Ya kuma ba mu labarin yadda ya ga jarabawar amanar maƙudan kuɗaɗe, da kuma mutane da abubuwan da ba zai taɓa manta ba, a tsawon shekarun da ya shafe a cikin wannan sana’a.
“Ofishin Ɗankabo Allah Ya jiƙan shi, jiragen da suka yi aiki can, kuɗin da aka tattaro daga Legas na wannan jigilar ta can, za a tattara su a kawo su Kano su kwana a ofishin Alhaji Falalu ƙanin Ɗankabo. In suka kwana nan da safe za a zazzage su nan a kan tebur ɗin shi Ciroma, Alhaji Falalu. Ina cikin yi masa yankan farce za a barni a ofis ɗin, daga inda Allah sai wannan kuɗin, su fita su je su yi wata harkarsu shi da abokan aikinsa su biyu, ni na uku, su bar ni Ni kaɗai sai wannan kuɗin, sai Allah.
“A nan ma nake ƙara gode wa Allah, ba a taɓa samun rafar da an ɗauki Naira biyar ba, a wannan lokacin Naira 20 ne manyan kuɗi. Ɗauri-ɗaurinsu ba a taɓa samun babu Naira 20 ko 40 ba, ko Naira goma-goma a ce babu ƙwaya biyu ko ƙwaya ɗaya ba, ba a taɓa samun haka a tattare da ni ba.
“Da haka nake gode wa Allah duk waɗannan hadarurrukaa iyafot, ban taɓa faɗawa ko guda daya ba. Allah ne Ya tsare ni Ya kare ni, kuma ina gode masa har yau har gobe.”
“An taba cewa sana’ar ba za ta riƙe mu ba, na je to mu ba mu raina ta ba.”
Kyan ɗa…
Da jin irin waɗannan nasarori da Alhaji Salihu ya samu a sana’ar yankan farce, sai muka tambaye shi ko a cikin ’ya’yansa akwai magajinsa, inda ya amsa da cewa, yana da ’ya’ya maza biyu, kuma kowanne ya iya kuma yana yi wa wansa, “amma ban taɓa ce wa waninsu lallai ya ɗauki kayan yankan farce ya fita cikin gari ba.”
Dattijon ya bayyana mana cewa ’ya’yan nasa “kownnensu yana da makama wadda ta fi ya saurari wannan ɗin, duk da cewa ni ina ganin babba ce wannan sana’ar, to amma su ba zan so su tsaya a kanta ba, na fi so su yi wata harka da ta wuce wannan ɗin, saboda canjin zamani.”
“Ni dai da Allah Ya ɗora wa abin kuma nake ganin albarkar abin, ina yi har yanzu, amma ina da buƙatar su wuce wannan matsayi,” in ji shi.
Sai mai haƙuri:
Ya ce sana’ar yankan farce ba kowa zai iya ba, sai mai haƙuri. “Za a kira ka a ce maka ka iya? In ka ce ka iya, amma ka yi wa mutum ka taɓa masa jiki, zai iya yi maka zagi ko wani wulaƙantci da ba ka zaci za a yi maka ba.
“Wani ya taba yi wa wani mutum yanka biyu. Mutumin yana ya zagin mai yankan farcen, aka kira ƙanina aka ce shi ya ƙarasa yankan farcen. Mutumin ya tafi ya ba su wuri.”
Alhaji Salihu ya ce wani mutum ya taɓa neman ya yi masa yankan farce, amma bayan kwana biyu da ya yi wa mutumin tuni sai ya ce, “ba zai biya ba sai mun je can (Lahira), na ce masa Allah Ya kai mu can. Daga nan ban qara yi masa maganar ba, yanzu an yi shekara 20.”
“Akwai wani abokina muna aiki a noma da shi muna maganar yankan farce sai ya ce, ya kamata in daina, ya taɓa ganin an yi wa wani ɗan sanda, ya kulle mai yi. Amma wannan bai sa na ji ɗar-ɗar na ji in daina ba.
“Tun daga wannan ya ba ni shawara in daina, kawo yanzu an kai shekara 30 da wannan magana. Kuma ban taɓa jin raina ya nuna min in fasa ba don na ji wannan maganar.”