Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce an yi wa Abdulkarim, dan Sanata Bala ibn Na’Allah, kisan gilla ta hanyar shake masa wuya da igiya.
Wannan ya saba da hasashe da ake yi a kafafen sa da zumunta cewa ’yan bindiga ne suka kashe babban dan na Sanata Na’Allah.
- Najeriya ta karbi ’yan gudun hijira 73,000 daga Kamaru
- Macron ya ziyarci tsohuwar cibiyar IS a Iraki
Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jihar cewa an samu gawar wani Kyaftin Abdulkarim, dan Sanata Na’Allah a gidansa da ke Kaduna.
“A wani abu mai kama da kisan gilla, an tsinci mamacin a cikin dakin kwana na gidansa da ke Malali, Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, a daure da igiya. Maharan sun sace wata mota daga wurin da yake ajiye motoci,” inji Aruwan.
Ya ce a wani lamarin, wasu ’yan bindiga sun kashe Ahmadu Tanko a Janwuriya a Karamar Hukumar Kajuru.
Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna matukar bacin ransa kan rahotannin sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu sannan ya aike da ta’aziyya ga iyalansu.
“Gwamna ya bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi don cafke wadanda suka kai harin kuma a halin yanzu jami’an tsaro suna bincike kan abubuwan da suka faru,” a cewarsa.