Wani magadanci mai yi wa kananan yara fyade da dubunsa ta cika ya ce yana yaudarar yaran ne da burodi da kudi N200.
Mutumin ya bayyana haka ne a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, inda ake zargin sa da zakke wa kananan yara masu shekara 10 zuwa 13.
- Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwanni saboda ’yan bindiga
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
- Yadda matasa ke Sahur da kayan maye a Azumin bana
Dubunsa ta cika ne bayan yaran da ya yi lalata da su a cikin shagonsa sun fallasa shi a ga iyayensu; Nan take kuma ’yan sanda suka cukuikuye shi zuwa ofishinsu.
Mutumin mai shekara 40 ya zakke wa biyu daga cikin yara, ya kuma yi wa ragowar biyun kwarkwasa a lokacin bikin Ista da bayan lokacin.
Magidancin mai ’ya’ya hudu da aka kama a Kafi-Koro da ke Karamar Hukumar Paikoro ta Jihar Neja, ya yi kaurin suna da aikata ta’asar.
A ma baya an taba gurfanar da shi bisa zargin lalata kananan yara a gaban Kotun Majistare ta 1 da ke Minna.
Ya shaida ’yan jarida a ofishin ’yan sandan cewa ya rudi yaran ne da kudi N200 da sinkin burodin da ya ba su a matsayin kudin yawon Ista.
Amma ya bayyana nadamarsa game da abin da ake tuhumar sa, amma mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da bincikar mutumin kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.