✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da an biya min kudin fansa, da na ajiye aikina – Kwamishinan Neja

“Ban kwato ni aka yi ba, kuma ba kudin fansa aka biya ba, kawai ikon Allah ne."

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja, Alhaji Muhammed Sani Idris wanda ya kubuto daga hannun masu garkuwa ranar Alhamis ya ce kubutar tasa wani ikon Allah ne kasancewar ko sisi ba a biya ba.

Ya kuma ce da gwamnati ta biya kudi kafin a sako shi da babu makawa yana dawowa zai sauka daga mukaminsa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da ’yan jarida a Minna, babban birnin Jihar ranar Juma’a, lokacin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt Hon. Abdullahi Wuse, wasu kusoshin gwamnatin Jihar da kuma iyalansa suka tarbeshi.

Da yake bayyana halin da ya kasance a hannun masu garkuwar, Muhammed ya ce shi kadai ne a hannun ’yan bindigar, inda ya ce duk da tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki, hakan bai sa ya karaya ba.

“Na shiga tashin hankali da kaduwa matuka. Na fito da daren ranar Alhamis, inda na kwana a asibiti domin a duba lafiyata, ranar Juma’a da safe kuma na karaso Minna cikin koshin lafiya.

“Ni kadai ne a hannun masu garkuwar inda su kace sun yi babban kamu kuma sun jima suna tsara hakan da mutane da kuma gungu daban-daban domin su kai ga gaci.

“Ban kwato ni aka yi ba, kuma ba kudin fansa aka biya ba, kawai ikon Allah ne.

“Da farko sun matsa min sosai, sun kai ni makurar da ban taba tunanin mutum zai iya sakkowa daga bisani ba. Amma na gode wa Allah saboda na yi imani da Shi, kuma sam ban karaya ba, na san Shi zai fitar da ni.

“Na tambaye su idan suna ganin abin da suke yi wanda Allah zai yi farin ciki da shi ne, sannu a hankali, a maimakon in karaya, sai ya kasance sune suka karaya, gwiwoyinsu suka fara yin sanyi.

“Daga bisani sai suka bani Burodi da Ruwa, suka kwance ni sannan suka bani wata leda guda daya da suke da ita domin na lulluba lokacin da ruwa ya sakko, su kuma suka tsaya a cikin ruwan.

“Daga nan suka fara bani kulawa, ni kuma na ci gaba yi musu nasiha, har daga karshe cikin ikon Allah suka sake ni suka ce in tafi gida,” inji shi.

Kwamishinan, wanda ya gode wa Gwamnan Jihar saboda yadda ya tsaya kai da fata a kan bakarsa cewa ba za a biya kudin fansa ba kamar yadda ya yi alkawari, ya ce yana matukar alfaharin kasancewa a kunshin gwamnatin Jihar mai ci.