Ina so a yi mini bayani a kan cutar da take kashe farata su yi baki suna molewa. Wasu na cewa tsutsar farce ce.
Daga Baba Lalo, Sumaila da Sunusi, Zarewa
Amsa: Akwai cutuka da dan dama da suke kashe farce. Wadansu farcen kawai sukan kama; wasu kuma duk jiki ciwon kan shafa har da faratan, kuma irin wadannan akan gano su, idan aka kalli farcen mutum.
Da farko dai akwai cutukan farce, su kansu, kamar a irin wadanda su farcensu ba ya fitowa ya yi tsawo waje, sai dai ya fito ya kuma lankwasa ya shiga fatar karkashin farcen ya yi ta girma a ciki, wanda ake kira ingrowing toenail, wanda hakan kan kawo zafi da radadi da lalacewar farcen.
Sa’annan akwai kwayoyin cuta, ba tsutsa ba, da kan iya shiga karkashin farce su kashe farcen. Irin wadannan akwai na bacteria masu kawo ciwon kakkare, wanda saboda tsananin radadi, nan da nan mutum zai nemi magani; akwai kuma na fungus masu kawo nannadewa da bushewar farcen shi ma ya mutu gaba daya. Da yake irin wannan na biyun ba wani zafi ne da shi ba, har kwayoyin su lahanta farcen mutum ba zai damu ba, wasu ma ba sa sani sai abu ya ci ya cinye, tsawon shekaru. Duka wadannan da zarar an ba da maganin kashe kwayoyin sun mutu, farcen ke ficewa, wani sabo ya fito.
Akwai kuma buguwa ta yau da kullum a jikin kofa misali ko da guduma a wurin sana’a, wadda kan sa datse jinin shi farcen. Shi ma saboda zafi, nan da nan mutum ke neman magani, amma saboda zubar jini karkashin farcen, dole dai sai farcen ya yi baki kuma ya mutu, daga bisani wani ya tsiro bayan ’yan watanni.
Akwai kuma cutukan cikin jiki gaba daya, wadanda kan taba lafiyar farce. Rashin isasshen jini a jiki, wanda muke kira anaemia da rashin wasu sinadaran bitamin, kan iya sa farce ya loba ciki, ya yi kamar cokali. Cutukan huhu kamar na tarin fuka da na dajin huhu da na zuciya su kuma kumbura farcen suke yi, da ma karshen yatsu gaba-daya. Cutukan borin jini masu karfi su kuma sukan tsattsaga farcen ne. Sigari kuma kan sa farcen duhu, kamar yadda takan sa fatar wasu duhu.
Wasu nau’ukan magunguna kamar na kashe ciwon daji sukan lahanta farata. Wasu kayan shafe-shafe da ado kamar lalle da jan-farce su kuma sukan ba farcen kala ne kawai ba tare da wani lahani ba. Idan mace na yawan sa irin wadannan, dole ta fada wa likita abin da ta shafa idan an zo duba lafiyarta.
Ko ma dai mene ne ya sa farcenka lalacewa da ka je wajen likitan fata ya gani ya san ko mene ne sanadi, kuma zai taimaka da yardar Allah.
Yawan tsabtar faratan kamar yanke su a kan lokaci da wanke su da hana yara yawo ba takalmi da cin abinci lafiyayyu sukan taimaka wajen rage cutukan farce.
Sauran Tambayoyi
Ni na kasance mai kiba kuma ina motsa jiki
kullum da safe, amma har yanzu ban ji canji ba. Ko akwai maganin da zan sha na ragu?
Daga M.M. Sultan
Amsa: Mai motsa jiki don rage kiba ana so a kalla ya rage kwatankwacin kilo guda cikin wata hudu, ko kilo uku cikin shekara. Don haka sai kana auna nauyinka akai-akai za ka gane kana raguwa ne ko kuma karuwa kake. Babu maganin rage teba a likitance, sai dai tiyatar rede tebar da ta taru a karkashin fata. Akwai dai wasu magungunan shigen irin wadanda kake magana, amma ba kiba suke ragewa ba, maikon cikin jini masu illa suke tsanewa, don haka ko da a fuska kana da kiba, idan aka auna maikon cikin jininka aka ga ba yawan da zai maka illa, ba za a rubuta maka su ba.
Ni ma ina da ’yar teba a ciki, nauyina kilo 55, shekaruna kuma 23. Ina son shawarar rage tebar.
Daga Khadija, Unguwar Rimi
Amsa: Nauyin kilo 55, komai tsayinki komai gajartarki, ba za a ce ya yi yawa ba. Hanyoyin rage tebar ciki da mara su ne na wani irin motsa jiki da ake yi a kwance rigingine, wato akan gadon-baya da daga kafafu ana saukewa, ko a sa musu wani nauyi ana dagawa, ko kuma tukin keke a iska, a kwancen, na tsawon mintuna ashirin a kullum; da dai sauran ire-iren motsa jiki da za su motsa tebar mara.
Ni kuma na je gwaji asibiti, an auna ni, an ce ina da ciwon hanta nau’in B. Ko za a ba ni shawarwari?
Daga Abubakar, Dukawuya
Amsa: Ya kamata ka san cewa akan samu kwayoyin ciwon hanta nau’in B ko dai daga wurin mahaifiya yayin da ake ciki ko yayin haihuwa, ko kuma daga abokiyar zama wato matarka, (wadda ita ma za ka iya sa mata idan ba ta da shi), ko kuma idan an taba maka karin jini a asibiti, jinin da ba a tantance lafiyarsa ba, ko kuma idan an taba yi maka amfani da kayan kaifin da aka riga aka yi wa wani mai cutar, kamar kaciya ko shayi, ko allurar kyamis da sirinji maras kyau da dai ire-irensu.
To idan ka san wadannan, ya kamata ka san cewa za ka iya sa wa wasu, kamar matarka da ’ya’yanta, don haka babbar hanyar kiyaye shafa wa wasu ita ce ta neman ’yar uwarka mai irin wannan matsala. Ana haka ne a asibitin da aka yi ma wancan gwajin, idan ka je ka yi bayani, kamar yadda yanzu a cibiyoyin karbar maganin sida akan hada mai cutar HIb da wata mai cutar a ba su shawara su auri junansu don kada su shafa wa al’umma.
Idan aka yi haka kuma idan ta samu juna biyu sai a je asibitin a ji ka’idojin kiyaye shi abin da ke ciki daga kwayar cutar, musamman idan an zo haihuwa da shayarwa, ciki har da allurar riga-kafin kamuwa da kwayoyin.
Sa’annan ya kamata ka san cewa, ba kamar HIb ba, shi wannan ciwo, yawanci, sai ka shafe rayuwarka bai nuna wasu alamu ba, kwayoyin na kwance, amma HIb kusan dole sai ta nuna kafin a je da nisa. Don haka ba wani magani da za ka nema na ciwon hanta na nau’in B a yanzu, domin har yau babu maganin kashe su. Idan ka fara jin wasu alamu na rashin lafiya, kamar kumburin ciki, zazzabi da canzawar kalar ido zuwa ruwan dorawa, to a iya cewa ciwon na hepatitis ya tashi, wato kwayoyin sun farka kuma suna hayayyafa. A wannan gaba akwai allurar kwantar da su, mai ’yar tsada wadda za ta iya sa ciwon ya lafa.
LAFIYAR MATA DA YARA
Amsoshin Tambayoyi
Ko akwai yadda mai juna biyu ya kamata ta rika kwanciya? Na ga idan ta kwanta a rigingine sai a ce ta tashi kada cibiya ta nade wa jariri wuya.
Daga Asma’u, Kaduna
Amsa: An fi so mace mai juna biyu ta rika kwanciya a gefe da gefe, ba rigingine ko rub-da-ciki ba. Idan tsohon ciki ne, sai a dan samu karamin matashi a sa a karkashin cikin ya dan tallafo shi, sai a dan ji dadi ta yadda nauyin ba zai rinjayi jiki ba. Da ma rub-da-ciki an san illarsa, amma rigingine ga mai juna biyu kan iya jawo ciwon baya ne, ba nadewar cibiya ba, domin nauyin jariri da mahaifa a kan gadon baya suke idan aka yi rigingine.
Nadewar cibiya a wuyan jariri kan iya faruwa haka kawai a kan kowa, tunda ko kin kwanta ko ba ki kwanta ba jariri motsinsa yake da buge-buge a ciki, wani ma shi yake nada wa kansa cibi bai sani ba. Yawanci nadewar cibiya a wuyan jarirai ba wata matsala ba ce ga jaririn in dai kwararriyar ungozoma ce ta karbi haihuwar a gida, ko kuma idan a asibiti aka haihu. Hannu kawai ake sawa a warware. Fitowar cibiyar kafin kan jariri ita ce matsala, wadda kan sa dole sai an yi tiyatar gaggawa.
Ni kuma ina so a fada mini lokutan da bakin mahaifa kan bude ko kuma ya rufe? Bayan al’ada da kwana nawa takan rufe?
Daga Mami, Kaduna
Amsa: Ba za a iya cewa takamaimai ga ranaku ko girman yadda bakin mahaifa kan bude ko ya rufe ba, domin kowace mace da irin tata kirar. Ya kamata dai ki san bakin a dan tsuke yake a koyaushe daidai gwargwado, amma ba a rufe ruf ba, domin shige da fice na wucewar ruwan mace na yau da kullum mai yaukin nan da kuma ruwan namiji mai kai ’ya’ya lokacin kwanciya. Yayin al’ada bakin kan kara budewa domin fitar jini. Haka ma yayin nakuda yakan bude a hankali kafin ya bude gaba daya don fitar jariri. Idan ya ki budewa a kan lokaci shi ma yakan iya jawo tiyatar ‘c.s.’ ta gaggawa.
Na yi hutun haihuwa na wajen shekaru bakwai, yanzu ina son na samu juna biyu, ko akwai gwaje-gwajen da sai na je an yi mini tukuna? A ba ni shawara.
Daga Jamila, Katsina
Amsa: A’a, ba wasu gwaje-gwaje a yanzu har sai an samu juna biyu. Da an ji alamu sai a je a tabbatar ta awon fitsari da hoto, sa’annan a fara zuwa awo. A sannan ne duk ake yin sauran gwaje-gwajen da suka dace.