✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Shan-inna ta sake bulla a Adamawa

Gwamnatin Jihar ta ce hakan babbar barazana ce.

Gwamnatin Jihar Adamawa ta tabbatar da sake bullar sabuwar nau’in cutar Shan-inna a Jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Farfesa Abdullahi Isa ne ya tabbatar da hakan yayin bikin kaddamar da allurar rigakafi zagaye na fako ranar Asabar a Yola, babban birnin Jihar.

Ya bayyana sabuwar nau’in cutar a matsayin mai rauni fiye da wacce aka fi sani a baya wacce take canzawa tsawon lokaci.

Kwamishinan ya bayyana matukar damuwarsa kan sake bullar cutar a Jihar inda ya ce hakan ba karamin kalubale ba ne a gare su.

“Mun sami rahoton bullar sabuwar nau’in cutar Shan-inna a Jiharmu.

“Hakan ba karamar barazana ba ce ga sake barkewar cutar a Jiharmu.

“Hakan ne ya sa ala tilas muka sake kaddamar da rigakafin cutar zagaye na farko ba tare da wani bata lokaci ba,” inji Kwamishinan.

Farfesa Isa ya kuma ce gwamnatin Jihar tare da tallafin kungiyoyin bayar da tallafi na kasa da kasa da Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun horar da ma’aikatan lafiya kimanin 800 domin su aiwatar da shirin allurar rigakafin.

Kimanin yara miliyan daya ne ’yan kasa da shekara biyar ake sa ran yi wa rigakafin a fadin Jihar.

Ita kuwa jami’ar WHO a Jihar, Misis Iyabosa Igbinovia ta tuno yadda a watan Agustan 2020 aka ba Najeriya shaidar kubuta daga cutar ta Shan-inna.

Sai dai ta ce sake bullar cutar a yanzu babbar barazana ce ba wai kawai ga Jihar ta Adamawa ba, har ma da ilahirin yankin Arewa maso Gabas.

“WHO na aiki kafada da kafada da gwamnatin Jihar wajen tabbatar da fattattakar cutar gaba daya tare da tabbatar da cewa dukkan yaran da suka cancanta a yi musu rigakafin, an yi musu ita” inji jami’ar. (NAN)