Jami’an lafiya uku da wani mara lafiya sun rasu sakamakon bullar cutar da ake zargin Zazzabin Lassa ce a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.
Wata majiya a asibitin ta ce daga cikin jami’an lafiyan da suka rasu har da wata mai yi wa kasa hidima (NYSC) da ake aiki a asibitin sojojin
Wata sanarwa da Mukaddashin Kwamandar Sashen Kiwon Lafiya na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya S.O Okoigo, ta ce, wasu karin mutane ma kwance cikin mawuyacin hali a sakamakon zazzabin Lassa da ake zargi.
“Wani mara lafiya da ma’aikata suka a Sashen Kula da Lafiya na Gaggawa a Asibitin Soji na 44 NARHK sun rasu, a yayin da wasu ke cikin mawuyacin hali,” inji sanawar da Birgediya S.O Okoigo, ya aike wa cibiyoyin lafiya na rundunar.
Ta ci gaba da cewa, jamia’an lafiyan sun rasu ne a garin jinyar mara lafiyan da ake zargi da cutar, “a tsawon kwanaki 10 da suka wuce, inda ya nuna alamar cutar kafin daga bisani rai ya yi halinsa.”
- Bayan mako 2: Abincin Tinubu ya kasa zuwa hannun ’yan Najeriya
- Za a rataye malamin addini kan fashin banki
Ya ce, “An rufe sashen kula da lafiya na gaggawan domin kashe kwayoyinc utar, sannan an tsaurara matakan kariya domin hana yaɗuwarta.
“An tura samfurin kwayar cutar zuwa cibiyar gwajin kwayar cuta ta Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da ke Kano, domin gudanar da bincike.
“An gayyato jami’an tantance kwayar cuta na Gwamnatin Jihar Kaduna domin gudanar da bincike sannan an dauki matakan kariya domin takaita yaduwar cutar.
“Haka zalika za a samar da alluran riga-kafi domin dakile yaduwar wannan cuta.”