Mutane kimanin 15 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan barkewar cutar Kwalara a kauyen Koya da ke Karamar Hukumar Minjibir ta Jihar Kano.
Haka kuma, an tabbatar da kwantar da mutum kimanin arba’in sakamakon cutar da har yanzu ba a gano musabbabin barkewarta ba.
- Yadda shirin ‘Dadin Kowa’ ke hana mata yin Sallar Asham
- Firaiministan Pakistan ya shiga dakin da aka binne Manzon Allah a Madina
Sulaiman Muhammad, mai garin kauyen wanda ya tabbatar wa da Aminiya ingancin rahoton, ya ce galibin wadanda lamarin ya ritsa da su mata ne da kananan yara da suka rika fuskantar amai da gudawa.
Kazalika, Sakataren Hukumar Lafiya a matakin farko na Jihar, Dokta Hussaini Tijjani, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawa da wakilinmu a ranar Lahadi.
Ya ce, tuni Ma’aikatar Lafiyar jihar ta tura tawagar kwararru zuwa yankin da abin ya shafa domin ba da agajin takaita yaduwar cutar.
Sai dai neman jin ta bakin Kwamishinan Lafiyar Jihar, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ci tura, yayin da bai amsa kiran wayarsa ba a lokacin tattara wannan rahoto.
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan da ya gabata ne wasu al’ummomi a Jihar Kano suka yi fama da wata bakuwar cuta sakamakon ta’ammali da wasu lalatattun kayan hada abun sha, inda akalla mutum goma suka rasu da kuma mutum kimanin mutum 200 da aka kwantar a asibiti.