Cikin fiye da mutum dubu uku da suka kamu da cutar amai da gudawa, an samu akalla mutum 119 da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar a fadin Jihar Kano.
Yayin ganawarsa da sashen Hausa na BBC, Mataimakin Daraktan Sashen Lafiyar Al’umma na Ma’aikatar Lafiyar Jihar, Dokta Bashir Lawan, ya ce an samu bullar cutar amai da gudawar a Kananan Hukumomin 33 daga cikin 44 da ke Jihar.
Dokta Lawan ya ce mutum sama da dubu biyu ne suka warke daga cutar a yayin da ake jinyar sama da mutum dari a Asibitoci daban-daban a fadin Jihar.
“Tun daga wuraren 5 ga watan Maris na bana kawo yau, 22 ga watan Yuni, mun samu mutum 3,209 wadanda suka kamu da wannan cuta, sannan mun samu mutum 2,996 da suka warke a yayin da akwai mutum 105 da ake kula da su Kananan Hukumomi daban-daban,” inji shi.
Babban Jami’in kiwon lafiyar ya ce Kananan Hukumomin Gaya da Bichi ne kan gaba wajen masu fama da wannan cutar, sai dai ya ce an samu raguwar masu kamuwa da cutar saboda matakan da Hukumomin Lafiya suke dauke wajen shawo kanta.
Daga cikin matakan da suka dauka kamar yadda Dokta Lawan ya wassafa akwai fadakarwa game da tsaftace kai da kuma muhalli.