Wani yaro dan shekaru bakwai da haihuwa, Ahmad Adam, da ke zaune a kusa da gidan Liman Sa’idu, Sabon Layi Funtuwa; wanda aka haifa da ciwo a kafarsa ta dama, yana neman taimakon Naira dubu dari uku da saba’in da biyar, domin yin maganin ciwon.
Aminiya ta tattauna da mahaifiyar yaron, Malama Umma Lawal ta waya, inda ta tabbatar da cewa ita ta haifi yaron shekaru bakwai da suka gabata amma ya zo da ciwo a kafarsa ta dama. Ta ce sun kai shi asibitoci a Funtuwa, inda aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu da ke Zariya, inda nan ma aka tura su Asibitin Koyarwa na Asibitin Malam Aminu Kano da ke Kano, inda suka gwada shi, suka ce za su yi masa aiki nan da mako hudu mai zuwa.
Ciwon kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, ya shafi cinyarsa da gwiwa da kuma gefen yatsunsa na kafa. Bayan da aka binciki yaron, an ce za a yi masa aikin tiyata da magani da sauran gwaje-gwaje da zai ci kudi har Naira dubu dari uku da saba’in da biyar.
Mahaifiyar yaron ta ce ba su da karfi da za su iya daukar nauyin aikin. Don haka ne take bukatar a taimaka masu don su ceci lafiyar wannan yaro. Ta ba da lambar wayarta, (07064471244) da lambar asusun ajiyarta na banki (Union Bank, 0056878535, Umma Lawal).
Majinyaci Ahmad Adam yana zaune ne da mahaifiyarsa bayan da suka rabu da mahiafinsa. Kuma ba ya iya zuwa makarantar Islamiyya ko ta boko saboda yara sukan firgita idan suka gan shi da kafa kumburarra.