Cristiano Ronaldo ya sake komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, shekara 12 bayan rabuwarsa da ita.
A ranar Juma’a kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sanar da cewa dan wasan ya nuna sha’awar barin ta.
- ‘Dalilin da Najeriya za ta mallaki hannun jari a Matatar Dangote’
- ‘Abin da ya sa muka kirkiri bikin Ranar Hausa’
Bayan daukar lokaci wakilin dan wasan, Jorge Mendes, yana kokarin kulla yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar Manchester City, cinikin bai kullu ba, a yayin da Manchester United ta shiga zawarcin dan wasan.
Manchester City ta janye daga cinikin ne bayan da ta fahimci cewa dan wasan ya fi sha’awar komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United.
A shekarar 2009 Cristiano Ronaldo ya bar Manchester United, ya koma Real Madrid kan kudi Yuro miliyan 80.
A 2018 kuma ya yi sallama da Real Madrid ya koma Juventus inda ya shafe shekara uku yana murza leda kafin yanzu ya yi bankwana da ita zuwa Manchester United.