Hukumar Lafiya ta Indiya ta ce cutar COVID-19 ta kashe sama da mutum 300,000 a kasar.
Wannan ya maida Indiya kasa ta uku da COVID-19 ta fi kashe mutane, bayan Amurka da Brazil, tun bayan sake bullarta a karo na biyu.
- An yanke wa dattijo lafiyayyar kafa aka bar mai ciwon
- EURO 2020: Babu dan wasan Real Madrid a tawagar Spain
- An kashe mutum 100 a kauyukan Binuwai
A ranar Litinin, Hukumar ta bayyana cewa mutum 4,454 ne cutar ta kashe a kasa da awanni 24, wanda ya sa adadin mutanen ta kashe kaiwa 303,720.
Wasu mutum 222,315 sun sake harbuwa da ita, wanda ya kawo adadin masu fama da ita a Kudancin nahiyar Asiya zuwa mutum miliyan 26.75.
Indiya ta zama kasa ta uku wurin yawan macu COVID-19 ne bayan Amurka mai mutum 589,893 da Brazil mai 449,068.
Masana kiwon lafiya a Indiya sun bayyana damuwa kan yadda mutane ke kin karbar rigakafin cutar, musamman a yankunan karkara.
A kasa da wata daya, Indiya ta fuskanci kalubale, inda mutum 100,000 suka mutu bayan harbuwa da cutar, bayan bullarta a karo na biyu cikin tsakiyar watan Fabrairun 2021.
Yawan masu mutuwa a dalilin cutar ya kawo cunkoso a asibitocin kasar, inda ake rasa gadajen kwantar da masu fama da ita.
Jami’ar Johns Hopkins, ta sanar da cewar COVID-19 ta harbi mutum miliyan 167, tare da kashe mutum miliyan 3.4 a fadin duniya.