Saudiyya ta dakatar da mutane daga wasu kasashe 20 shiga kasarta, a sabon yunkurinta na hana yaduwar cutar COVID-19 a karo na biyu.
Sanarwar daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta ce umarnin Masarautar zai fara aiki ne daga ranar Laraba da dare.
- An killace ’yan Najeriya 384 da aka kwaso daga Saudiyya a Abuja
- Za a kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Saudiyya
- Sojojin Saudiyya sun dakile harin mayakan Houthi
- COVID-19: Saudiyya ta sake bude tashoshin jirage
“Matakin da aka dauka kan kasashe 20 din ya biyo bayan umarnin da Masarautar ta bayar.
“Duk dan kasar Saudiyya da ya fito daga kasashen zai shigo Saudiyya ne bisa matakan kariyar COVID-19,” inji sanarwar.
Rahotanni sun bayyana cewa jerin kasashen da Saudiyya ta dakatar din su ne: Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Turkiyya, Japan, Indiya, Pakistan, da Sweden.
Sauran su ne: Ajantina, Daular Larabawa, Indonisiya, Ireland, Brazil, Portugal, Afrika ta Kudu, Switzerland, Lebanon, Masar.