Cibiyar Ci gaban Al’umma da Bincike (CCDRN) ta kaddamar da shirin tallafawa mutane 2,230 daga Kananan Hukumomi shida a jihar Kano.
Daraktan kungiyar Abba Isyaku ne ya bayyana hakan, inda ya ce shirin zai mayar da hankali ne wajen tsaftar muhalli.
Ya ce, “Daga cikin mutane 2,230, guda 1,600 za su yi aikin tsaftar muhalli a Kananan Hukumomi shida mu biya su.
“Ragowar kuma za su yi aiki don tabbatar da bin matakan kariyar COVID-19 a makarantun da aka ware a Kananan Hukumomin Gwale, Dala, Birni da Kewaye, Ungoggo, Fagge da Kumbotso,” cewar Isyaku.
Daga nan sai ya kuma ce wasu daga cikin wadanda za su ci moriyar shirin za a kai su asibitoci don taimaka wa da tsabtar muhalli.
Ya ce wanda suke kan wannan tsari za a rika biyansu kudi Dalar Amurka 80 (38,400) har na tsawon watanni uku.
Sai dai ya ce akwai kashi na biyu na wanda su ma za a tallafa musu, wato wadanda cutar Coronavirus ta durkusar da kasuwancinsu.
Ya ce mutane 630 za a tallafa musu da Dalar Amurka 300 (144,000), don habaka kasuwancinsu.
Daraktan ya ce wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da kuma kungiyar.
Da yake jawabi, Mai Taimakawa Gwamnan Kano na musamman kan Cimma Muradun Karni, Habib Hotoro, ya ce jama’a za su amfana da shirin yadda ya dace.
Ya kara da cewa jami’an gwamnati za su sanya ido tare da yin rangadi kowanne wata don tabbatar da wadanda aka dauka na aikinsu yadda ya kamata.