Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi jama’a da su kiyayi ’yan damfara da ka iya amfani da yanayin da aka shiga sakamakon barazanar annobar coronavirus su yi masu sakiyar da ba ruwa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito daraktan yada labarai na bankin, Isaac Okorafor, yana cewa ’yan damfara na amfani da wasu dabaru don sace bayanan da za su ba su damar kutse cikin kwamfiyuta ko wayoyin mutane.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Mista Okorafor ya ce bata-garin sun kirkiri wata taswirar kasashen da ke fama da coronavirus suna satar bayanan mutane ta karkashin kasa.
Bayan wannan kuma, a cewar Okorafor, ’yan damfarar kan aike da sakwannin email da sunan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ko Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) dauke da rariyar likau (wato link) wadda idan mutum ya latsa za a sace bayanan sirri da ke kwamfiyuta ko wayar salularsa.
Bugu da kari, a cewar jami’in, barayin bayanai kan aike da sako ta kafofin sadarwa na zamani (social media) cewa gwamnati ko wasu kungiyoyi na bayar da tallafi, a je wani shafin intanet a yi rajista; amma a fakaice wannan wata hanyar yaudara ce ta satar bayanan mutane.
Ya kara da cewa wani lokaci ma ’yan damfarar kiran mutane suke yi a waya su bukaci lambobin tabbatar da sahihancin asusunsu na banki (BVN).
Mista Okorafor ya yi kira ga ’yan Najeriya cewa yayin da suka mayar da hankali wajen yakar cutar coronavirus to kada su shagala su bari a yaye abin da suke taskacewa na bayanai da ma tsabar kudi.
Tun bayan da hankali ya koma kan annobar coronavirus ne dai ake ta yada sakwanni iri-iri a kafofin sadarwa na zamani a kan hanyoyin kariya ko na samun tallafi.