Shugaban karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Abdulrahman Sani-Maigoro, ya ce karamar hukumar ta mayar da wasu matafiya su tara da suka fito daga jihar Kano wadanda aka tsare a garin Keffi a ranar Talata.
Sani-Maigoro ya bayyana cewa karamar hukumar ta dauki matakin ne saboda dokar da gwamnatin jihar ta kafa a kokarin dakile cutar coronavirus.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake jawabi wa manema labarai.
Ya kuma kara da cewa karamar hukumar ta tsare motoci shida dauke da fasinjoji daga jihohin Kano da Legas kuma tuni ta mayar da su inda suka fito.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da labarin da yake yaduwa a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta cewa ‘yan kasuwa masu fataucin yadi suna ci gaba da tafiye-tafiye daga Kano zuwa Keffi.
“Rahoton wanda wadansu mutane suka dauki nauyin yada shi basa nufin karamar hukumar mu da kuma jiharmu baki daya da alheri. Labarin na kanzan kurege ne” Inji shugaban karamar hukumar.
Ya yi kira ga masu yada irin wadannan labaran da su matso su hada hannu da shi saboda dakile cutar da kuma samar da ci gaba a kasar.
“Na yi iya kokarina kuma zan ci gaba da yi saboda ina da kwamiti na musamman suna sa ido a kan hanyoyi da ke zuwa sauran jihohi saboda magance yaduwar annobar.
“Na kafa kwamiti da zai yi aiki ba dare ba rana saboda tabbatar da cewa al’umma sun yi biyayya ga dokar da gwamnati ta kafa.
“Za a iya ganin haka a kan tsare fasinjoji tara a wata mota kirar Sharon da ta taso daga Kano ranar Talata wadanda muka mayar da su inda suka fito”, inji shi.
Maigoro ya nemi mazauna yankin da su ci gaba da bin umurnin gwamnati da na kwararru kan kiwon lafiya saboda yaki da cutar coronavirus.