Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya tsawaita dokar zaman gida da ta kafa da nufin kauce wa yaduwar cutar Coronavirus da kwanaki 30, sannan ta kara mata tsanani.
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan shawarar da Kwamitin Yaki da Cutar ta Coronavirus a jihar wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ke shuganta suka bayar ne.
Ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadin nan 26 ga watan Afrilu.
Ya kuma sanar da hakan ne a wata sanarwa dake dauke da sa hannun mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai watau Muyiwa Adekeye wadda kuma aka rabawa manema labarai.
Sannan kuma gwamnatin ta ce kwanaki biyu da take bai wa mutane suna fita domin zuwa sayen kayan abinci yanzu ta mayar da shi kwana daya rak a mako.
Ya ce ganin yadda ake ci gaba da samun yaduwar wannan cuta a jihohi makwabta da kuma Abuja; kuma duba da cewa tafiye-tafiye na cikin hanyoyin yada cutar, kwamitin na ganin idan har ana da bukatar kare al’ummar jihar dole sai an dauki matakai masu zafi.
“Kwanaki biyu da ake barin mutane suna fita sayen abinci watau Talata da Laraba an mayar da shi kwana daya tak.
“Daga yanzu ranar Laraba kadai za a rika barin mutane suna fita har sai an samu saukin cutar.
“Kuma duk wanda ya fito daga gidansa da nufin shiga gari dole sai ya sanya abin rufe baki sannan ya rika kaucewa cunkoso a duk inda yake a cikin kasuwa ko a cikin motarsa.
“Gwamnati na kokarin ganin yadda za ta samar da kyallen rufe fuska domin raba wa talakawa. Sannan ta yi kira ga wayanda ke da hali da su samu telolinsu su dinka masu na yadi wanda za su iya wankewa idan ya yi dauda.
“Gwamnatin ta kuma nemi teloli da su dinka kyallen rufe fuska domin saida wa jama’a. Domin za a tilasta rufe fuska a wani yunkuri na hana yaduwar cutar a tsakanin mutane,” inji sanarwar.
Gwamnatin ta ce a bisa dokar kasa da take amfani da ita, daga yanzu kowa zai rika zama a gida, ba fita waje—babu zuwa ofis, ko biki, ko kasuwa, ko wurin ibada.
Sanarwar ta kuma ce sai wadanda doka ta amince masu da su fita kadai kamar jami’an kiwon lafiya da jami’an tsaro da na kashe gobara da ma’aikatan ruwa da wutar lantarki da masu aiki na musamman za a kyale.
Masu tankar man fetur ma doka ta yarda masu su fita, amma da sharadin ba za su debi fiye da mutum uku har da direba ba.
Masu sayar da abinci da magunguna an yarda za su bude su gudanar da harkokinsu. Amma makarantu da wuraren ibada da otal-otal da filayen wasanni da duk wani wuri dake tara jama’a duk ba a son ganin su a bude.
Su kuwa masu keke mai kafa uku, wadanda aka fi sani da keke NAPEP, da motocin da ake amfani da su wajen shigo da jama’a a boye za a kama su a kwace motar muddin aka samu mutum da laifin karya dokar.
Sanarwar ta kuma ce duk wanda aka kama zai shiga jihar, ko zai wuce zuwa wata jihar mai makwabtaka, to za a ba shi zabi: ko dai ya koma inda ya fito ko kuma a killace shi har tsawon mako biyu.
Gwamnatin ta nemi jama’a da su ci gaba da bin dokoki da shawarwarin masana kiwon lafiya domin a samu saukin wannan annoba.