✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Bana babu gasar Ballon d’Or

Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta sanar da cewa bana ba za ta fitar da Gwarazan ’Yan Wasan bana wanda ake fi sani da Ballon d’Or…

Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta sanar da cewa bana ba za ta fitar da Gwarazan ’Yan Wasan bana wanda ake fi sani da Ballon d’Or ba saboda annobar coronavirus.

Hukumar ta ce an dakatar da bikin ne kasancewar annobar ta shafi harkokin kwallon kafa a duniya.

Ta ce annobar ta hana a samu damar natsuwa a bibbi ka’adodi da sharudan lashe gasar, wanda hakan ya sa dole a dakatar da fitar da gwarazan na bana.

An fara ba da wannan kyautar ce a shekarar 1956, kimanin shekara 64 ke nan.

Wannan ne karo na farko da ba za a bayar da kyautar ba a tarihinta.

Dan wasan Ajantina da Barcelona Lionel Messi ne ya fi kowa lashe kyautar, inda yake da guda shida, sai Cristiano Ronaldo da ke biye masa da guda biyar.

Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ce ke daukar nauyin bayar da kyautar ballon d ‘or.

A tsakanin shakarar 2010 da 2015, an gwama gasar da ta FIFA, wadda aka fara a shekarar 1991, inda kyautar ta zama FIFA ballon d‘or, sannan daga bisa aka sake rabewa.

A yanzu haka Lionel Messi ne ke rike da kambun, kuma dage gasar ta bana na nufin a karon farko, mutum daya zai yi shekara biyu rike da kambun.

%d bloggers like this: