✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 An sake rufe wasu kananan hukumomin Katsina 

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sake bayar da sanarwar sake rufe wasu kananan hukumomi uku a jihar Katsina sanadiyyar cutar coronavirus. Kananan hukumomin…

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sake bayar da sanarwar sake rufe wasu kananan hukumomi uku a jihar Katsina sanadiyyar cutar coronavirus.

Kananan hukumomin da aka rufe sun hada da: Karamar hukumar Katsina da Daura da Batagarawa wadda take makwabta da Katsina.

Kamar yadda Gwamnan ya ce, daga cikin mutane 337 da aka samu dauke da cutar, karamar hukumar Katsina na da mutum 215, yayin da Daura nada mutum 79.

Da farko an bude kananan hukumomin ne domin bayar da damar yin shirye-shiryen bukukuwan karamar Sallah. Daga bisani aka samu Karin adadin masu dauke da cutar.

Ba a dai sanar da kwanakin da za a bude kananan hukumomin ba.