Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umarnin hana fita kwata-kwata a karamar hukumar Katsina daga karfe 7.00 na safiyar Talata.
Matakin ya biyo bayan samun wasu mutane biyu ne da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a karamar hukumar.
Gwamna Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka yanzun nan ga manema labarai a Gidan Gwamnati da ke Katsina, babban birnin jihar.
Sai dai a cewar gwamnan akwai wasu wuraren sayar da abinci da aka dauke wa dokar, bankuna an ba su dama su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba, sannan masu larura ta musamman za su iya fita domin neman mafita.
Gwamnan ya kuma yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya, musamman wadanda ke kan iyaka, su sa ido sosai don tabbatar da cewa ba wanda ya saci jiki ya shiga jihar.
Wannan mataki dai ya kawo adadin kananan hukumomin da aka ba da umarnin hana fita a jihar zuwa uku.
Gwamnatin dai ta ce ba za ta rufe jihar gaba daya ba, amma duk karamar hukumar da aka samu wanda aka tabbatar ya kamu za a kaa mata doka.