Mutum uku da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Sakkwato sun rasu.
Gwamnan jihar ta Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwar rasuwar mutanen ta hannun mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai Muhammad Bello.
Mutanen uku. a cewar gwamnan, suna fama da wasu larurori daban-daban kamar ciwon suga da asma da hawan jin kafin cutar ta coronavirus ta kama su.
Sanarwar dai ba ta ambaci sunayen wadanda da suka rasu ba, amma wani bayani da Aminiya ta samu ya nuna cewa a cikin mutanen akwai Sahabi Masau, wani dan sanda da ya dade yana aiki a fadar gwamnatin jihar kafin cutar ta kama shi a makon da ya gabata.
- An samu mai cutar coronavirus na farko a jihar Sokoto
- Tawagar shugaban kasa ta musamman ta sauka a Kano
Majiyar ta tabbatar wa Aminiya cewa kafin rasuwarsa yana cikin makusantan gwamna daga cikin jami’an tsaron da ke fadar gwamnatin jiha.
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya na baya-bayan nan dai sun nuna cewa mutum 19 aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Sakkwato.