✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus ta yi ajalin likita a jihar Katsina

Wani likita ya rasu a jihar Katsina sakamakon kamuwa da cutar coronavirus. Da yammacin ranar Talata ne gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya bayar da…

Wani likita ya rasu a jihar Katsina sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

Da yammacin ranar Talata ne gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya bayar da sanarwar mutuwar likitan mai zaman kansa mai suna Dakta Aliyu Yakubu.

Dokta Yakubu, wanda dan kabilar Igala ne, ya mutu a asibitin sojojin sama da ke Daura bayan shi da kansa ya je saboda rashin lafiyar da ke damun shi.

Likitan bai dade da dawowa daga Legas ba.

An kuma ce sai da ya fara zuwa jihar Kogi kafin daga bisani ya je Legas din.

Marigayin, wanda ya mutu tun ranar Asabar, an debi jininsa domin gwaji.

Sakamakon dai ya fito ne da yammacin ranar Talata yana nuna cewa Dokta Yakubu na dauke da cutar Coronavirus wadda ta yi ajalinsa.

Gwamna Masari ya ce tuni aka kai kwararrun likitoci Daura domin gano wadanda ya yi ma’amula da su bayan dawowarsa daga Legas.