Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bayar da umarni a yi wa dukkan kwamishinoni da sauran ‘yan majalisar zartarwarsa gwajin coronavirus su kuma killace kansu, bayan kamuwa da cutar da kwamishinan ciniki da masana’antu, Mista Abe Aku, ya yi.
Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne, da yammacin ranar Laraba kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kwamishinan yada labaran jihar, Mista Dan Manjang, ta nuna.
“Domin cika wannan umarni da gwamnan ya bayar, za a dauki samfurin kwamishinonin da sauran ‘yan majalisar zartarwar jihar a tura zuwa cibiyar binciken cututtuka ta kasa da ke Vom”, inji Mista Manjang.
Sanarwar ta kuma shawarci jama’a su guji ziyartar kwamishinonin da ‘yan majalisar zartarwar, a yayin da suka killace kansu.
Sai dai babu bayani a cikin sanarwar a kan ko gwamnan ma zai killace kansa, sannan shi ma a sake yi masa gwaji.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne aka yi wa gwamnan da iyalinsa gwajin wannan cuta, kuma sakamakon da ya fito ya tabbatar ba sa dauke da ita.
A wata sabuwa kuma kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Nimkong Lar, ya bayyana cewa mutum takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta a jihar Filato, yayin da mutum hudu da aka tabbatar suna dauke da ita suka tsere daga inda ake yi masu jinya.
Har ila yau, kwamishinan ya ce zuwa yanzu mutum 330 ne suka kamu da wannan cuta, a jihar ta Filato, kuma 41 daga cikinsu ma’aikatan kiwon lafiya ne.
“Mutum 156 ne da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta a jihar suka warke kuma tuni an sallame su sun koma cikin iyalansu”, inji Dokta Lar.
Ya kuma ce mutum 4,076 ne aka yi wa gwajin wannan cuta a jihar kuma an samu sakamakon mutum 3,471, yanzu ana jiran na mutum 605.
Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya umarci a yi wa ‘yan majalisar zartarwarsa gwajin coronavirus su kuma killace kansu, bayan kwamishinan ciniki da masana’antu, Abe Aku, ya kamu da cutar