Jama’a a Jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba sun samu damar walwala bayan rage yawan lokutan hana fita da gwamnati ta yi.
Masu ababen hawa da kekune masu kafa uku da motocin haya duk sun hau tituna, sannan an bude kasuwanni da sauran wuraren kasuwanci a ciki da wajen babban birnin na jihar Taraba.
An dai rage dokar hana fitar ne ta yadda daga ranar Alhamis aka bai wa jama’a dama su fita daga karfe 8.00 na safe zuwa karfe 2.00 na rana.
Babban sakataren watsa labarai na gwamnan Jihar, Mallam Hassan Mijinyawa, ya bayyana cewa gwamnan ya rage dokar ne bisa la’akari da irin kunci da takura da ta haifar.
Shi ma da yake nuni da cewa daukar wannan mataki ba zai yi kafar ungulu ga yunkurin hana cutar yaduwa ba, kwamishinan lafiya na jihar Dokta Innocent Vakkai ya ce har zuwa yanzu ba a samu wanda ya kamu da cutar coronavirus ba.
“Gwamnatin jiha za ta ci gaba da aiwatsr da dukkan matakan da za su hana yaduwar cutar” inji Dokta Vakkai.
Ya kara da cewa za a ci gaba da nazarin fa’idodin dokokin da aka gindaya.
Da yawa daga cikin wadands wakilin Aminiya ya zanta da su a kan rage lokutan hana fita a jihar sun nuna gamsuwarsu Kan rage yawan lokutan hana fita da gwamnatin Jihar tayi.
Daya daga cikin su mai suna Mallam Tanko Sanusi ya ce dokar ta kawo wahala ga jama’a, musamman marasa karfi.
“Gwamnati ta hana jama’a fita kuma ba ta tanadi komai ta ba su ba kamar yadda wasu gwamnatocin suka yi”, inji shi.