Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umarnin dakatar da sallar Juma’a a daukacin masallatan Juma’a na jihar daga makon gobe.
Sakataren Gwamnatin Jihar Mustapha Inuwa, wanda ya bayyana hakan, ya ce Gwamna Aminu Bello Masari ne ya ba da umarnin.
Bugu da kari, gwamnan ya ba da umarnin dakatar da Tafsiri da sallar Asham a watan azumi a dukkan masallatai da wuraren taruwar jama’a a fadin jihar.
Wannan umarni dai ya biyo bayan samun wani da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus ne a karamar hukumar Dutsin-ma.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin hana fita a karamar hukumar ta Dutsin-Ma daga karfe 7 na safiyar yau Juma’a.
“Wani rahoto daga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ya tabbatar da cewa an samu wanda ke dauke da COVID-19 a garin Dutin-ma, lamarin da ya sa dole a rufe karamar hukumar don hana cutar yaduwa zuwa wasu sassan jihar”, a cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato daga sakataren na gwamnatin jihar Katsina.
Bayan haka kuma, Gwamna Masari, inji sanarwar, ya ba da umarnin rufe kasuwannin da ke ci mako-mako a fadin jihar.
Kasuwannin dai su ne Mai’adua, da Mashi, da Charanchi, da Dandume, da Zango, da Danja, da Bakori, da Kaita, da Kagadama, da kuma Dankama.
Haka kuma an ba da umarnin rufe dukkan gidajen kallon wasa da na sinima a fadin jihar.
“Ya zama wajibi a yi biyayya ga wannan haramci daga ranakun da aka ayyana har sai abin da hali ya yi”, inji sanarwar.
Dutsin-ma ce karamar hukuma ta biyu da gwamnatin jihar Katsina ta kallafawa dokar hana fita, baya ga Daura.
Zuwa yanzu dai an tabbatar da jihar na da mutum shida da suka kamu da cutar coronavirus, daya daga cikinsu kuma ya riga mu gidan gaskiya.