Kungiyar Direbobin Motocin Haya ta Jihar Taraba ta nemi gwamnatocin tarayya da na jihohi su tallafa wa ‘ya’yanta.
Shugaban kungiyar na shiyyar Jalingo, Alhaji Inuwa Garba, shi ya yi wannan kiran yana mai cewa umarnin da aka bai wa direbobi su rage yawan fasinjojin da suke dauka don takaita yaduwar cutar Coronavirus zai shafi rayuwarsu.
A cewar Alhaji Inuwa, duk da bin wannan umarni da direbobin suka yi ba su kara kudin mota ba, don haka ba za su tsira da komai ba.
A karkashin sabuwar dokar, inji shugaban direbobin, motar haya da ke daukar fasinjoji goma ta koma daukar fasinjoji shida zuwa bakwai,
“Muddin ba a tallafa wa direbobin motocin haya ba, to za a wayi gari direbobi ba za su iya gudanar da ayyykan su ba domin ba riba”, inji shi.
Ya kara da cewa ya zama tilas gwamnati ta bai wa direbobin motocin haya tallafi domin cike gibin fasinjoji da aka ragewa direbobi dauka a wannan lokacin da ake fuskantar matsalar yaduwar cutar coronavirus.