Kafofin yada labarai mallakar hukumomin China sun mayar da kakkausan martani ga Amurka suna zargin gwamnatin Shugaba Donald Trump da yunkurin kau da hankali daga “rashin kwarewarta” ta hanyar zarge-zarge game da yaduwar cutar coronavirus.
Wani sharhi da aka wallafa ranar Litinin a jaridar Global Times, wadda ake bugawa a karkashin inuwar jaridar People’s Daily ta Jam’iyyar Kwaminis ta China, ya yi watsi da zargin cewa China ta yi rufa-rufa game da girman matsalar coronavirus, yana mai cewa ba hi da tushe balle makama.
Jaridar ta ce ikirarin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo cewa hukumomin leken asiri na binciken wata hujja da ke nuna cewa daga wani dakin bincike a Wuhan kwayar cutar ta fito cika-baki ne kawai.
- Iran ta zargi Amurka da kitsa yaki a duniya
- An bude makarantu a China bayan sassauta dokar hana fita
“Gaskiyar magana ita ce Pompeo ba shi da wata hujja; idan kuwa har Amurka tana da wata kwakkwarar hujja, to ta ba cibiyoyin bincike da masana kimiyya su yi nazari su tabbatar da ita.
“Burin gwamnatin Amurka shi ne ta dora alhakin yaduwar annobar a kan China ta kuma juya wa mutane tunani don kada a zarge ta da aikata ba daidai ba”, inji jaridar.
Ta kuma kara da cewa babban burin Shugaba Trump a yanzu shi ne ya ci zabe ya koma wa’adi na biyu a kan mulki a watan Nuwamba.
A halin da ake ciki kuma, Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato kafofin yada labarai na Canada suna cewa Fira Minista Justin Trudeau ya ce ya yi wuri a hakikance bayanan da ke cewa coronavirus ta samo asali ne daga wani dakin bincike a China.
Canada dai mamba ce ta Five Eyes, wani kawancen kasashe ta fuskar leken asiri da ya hada da Amurka da Burtaniya da Canada da New Zealand da kuma Australiya.