Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta samu tikitin zuwa matakin kusa da na karshe a gasar Copa Del Rey bayan doke Real Sociedad da ci daya mai ban haushi.
Dan wasan gaban Barcelona, Ousmane Dembele ne ya zura kwallo daya tilo a raga a minti ma 54.
Real Sociedad ta samu koma baya a wasan, bayan da alkalin wasa ya bai wa dan wasan tsakiyarta, Braiz Mendez jan kati a minti na 40 da fara wasan.
Hakan ya sanya kungiyar ta daina kai hare-hare tare da tarewa a gida don tare farmakin da Barcelona ke kai mata.
Sai dai ba jimawa da dawowa daga hutun rabin lokaci, Dembele ya saka Barcelona a gaba.
Akalla mutum dubu 85 ne suka shiga filin wasa na Camp Nou don kallon wasan.
Barcelona na ci gaba da jan zarenta a bana, bayan ta lashe kofin Super Cup a hannun Real Madrid, wadda ta doke da ci 3 da 1 a Saudiyya.
Kazalika Barcelona na ci gaba da jan ragamar teburin Gasar Laliga ta Sifaniya da maki 44 daga wasa 19, yayin da Real Madrid ke biye mata a baya da maki 41 daga wasa 19.