✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Copa America: Jibi Brazil za ta yi wasan karshe da Peru

A Jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasan karshe na cin kofin Kudancin Amurka da aka fi sani da Copa America.…

A Jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasan karshe na cin kofin Kudancin Amurka da aka fi sani da Copa America.

A bana ana gudanar da gasar ce a kasar Brazil kuma za a yi wasan karshen ne a tsakain mai masaukin baki da kuma kasar Peru.

Kafin Brazil ta kawo wannan mataki sai da ta doke Ajantina da ci 2-0 a ranar Talatar da ta wuce yayin da Peru ta lallasa Chile mai rike da kofin da ci 3-0.

Abin sha’awa shi ne wannan shi ne karon farko da Peru za ta buga wasan karshe tun bayan da ta dauki kofin a shekarar 1975 kimanin shekara 46 da suka gabata.

Tarihin gasar ya nuna kasar Uruguay ce ta fi yawan daukar wannan kofi inda ta dauka sau 15 sai Ajantina ke biye inda ta dauka sau 14.  Sai dai rabon da Ajantina ta dauki kofin tun a shekarar 1993 kimanin shekara 26 da suka wuce.

Brazil ce ta uku inda ta dauka sau 8, kuma ta dauki na karshe ne a shekarar 2017.

Don haka wasan karshen zai yi armashi ganin Brazil da Peru suna kokarin lashe kofin ne don shiga kundin tarihi.