A ranar Alhamis Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG, ta kaddamar da gwagwarmayar neman a ceto daliban Makarantar Sakandaren kwana ta garin Kankara da aka sace a makon da ya gabata.
Gamayyar kungiyoyin sun kaddamar da gwagwarmar mai taken #BringBackOurBoys da zummar yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatinsa matsin lambar ganin an ceto daliban cikin hanzari da kuma neman a tunkari matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
- Tambuwal ya bayar da umarnin rufe makarantun kwana 16 a Sakkwato
- Gwamnatin Katsina ta karyata labarin sako Dalilan Kankara
- Gwamnonin APC sun taya Buhari murnar cika shekaru 78 a duniya
Sai dai kungiyar bisa la’akari da yanayi na rashin tsaro ta jingine zanga-zangar lumanar da ta yi niyyar gudanarwa a birnin Katsina da kuma Daura da ta kasance mahaifar Shugaban Kasa Buhari.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bakin Babban Jami’in Gudanarwarta na Kasa, Balarabe Rufa’i, dangane dalilin jingine zanga-zangar, ta ce Gwamnatin jihar ta ba ta tabbacin kubutar da daliban cikin kankanin lokaci a yayin da take ci gaba da tuntubar wadanda suka sace su.
Mista Rufa’i ya jaddada cewa kungiyar ba za ta dauke kafa kuma za ta ci gaba da wannan gwagwarmaya babu kakkautawa har sai an dawo da dukkan daliban da aka sace a raye kuma cikin koshin lafiya.
Kazalika CNG ta aike wa gwamnatin Katsina wasika domin ta isar da sakonta na nuna bacin rai ga Shugaba Muhammadu Buhari dangane da mummunan yanayi na rashin tsaro da ya yi wa Najeriya dabaibayi.
Ta kuma yaba wa gwamnatin jihar kan jajircewar da ta nuna wajen ganin an ceto daliban tare da nuna takaicinta kan abin da ta kira gazawar Gwamnatin Tarayya.
“Ga dukkan alamu Gwamnatin Tarayya ta gaza a yayin da ta nuna rashin damuwa wajen daukar matakan ganin an ceto daliban cikin hanzari duk da mawuyancin halin da suka tsinci kansu a ciki na rashin samun lafiyayyen abinci, tashin hankalin rabuwa da ’yan uwansu da kuma barazanar rasa rayukansu.”
Da yake karbar wasikar a madadin Gwamnatin Jihar Katsina, mai baiwa gwamna jiihar shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina, ya tabbatar wa da kungiyar cewa za a isar da sakonta tare da jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da yin iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da daliban cikin aminci.