✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon daji na kashe mata 26 kullum a Najeriya  —Zainab Bagudu

Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana cewa mata 26 ne kullum ke mutuwa a Najeriya sakamakon ciwon daji na wuyan mahaifa…

Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana cewa mata 26 ne kullum ke mutuwa a Najeriya sakamakon ciwon daji na wuyan mahaifa wato Cervical Cancer.

Dokta Bagudu ta ce Najeriya ta kere sauran kasashe a Afirka samun mata masu mutuwa a dalilin cutar ta sankarar mahaifa.

“Ina rokon iyayenmu musamman sarakuna da su taimaka mana wajen yaki da ciwon daji.

“Sama da mata miliyan 36.59 ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar daji a duniya kuma mata 26 ne ke mutuwa kullum a Najeriya a dalilin ciwon”, cewar Dokta Bagudu.

Ta bayyana hakan ne a taron Ranar cutar Shan-inna ta Duniya da aka gudanar a Karamar Hukumar Argungun da ke Jihar Kebbi.

Cikin wani rahoto da BBC ta wallafa a bara, Dokta Zainab ta ce masana sun gano cewa cutar ta fi tsanani a Arewacin Najeriya saboda yawan haihuwa

Sobada haka ta yi kira da mata su rika takaita haihuwa ta hanyar rungumar tsarin ba da tazarar iyali.

A baya-bayan nan ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta cire Najeriya daga cikin kasashe masu fama da cutar shan-inna.