Manchester City ta casa Liverpool da ci 4-1 a wasan mako na 29 da suka fafata ranar Asabar a filin wasa na Etihad.
City ta yi nasarar ce duk da rashin zakakurin dan wasanta na gaba Erling Haaland.
- Gobara ta lakume rayuka biyu da gidaje 500 a Borno
- An kama mutumin da ya yi barazanar gayyatar ’yan awaren IPOB zuwa Legas
Haaland – wanda ya ci wa Man City kwallo 42 a kakar wasa ta bana – yana fama da rashin lafiya.
Sai dai, duk da haka kungiyar ta nuna irin karfin da take da shi bayan ta farke kwallon da Liverpool ta fara jefa mata a raga.
City mai kwantan wasa daya ta soma wasan da tazarar maki takwas a bayan kungiyar Arsenal da Mikel Arteta ke jagoranta, kuma ta fuskanci koma baya tun kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan Mohamed Salah ya sakada mata kwallo.
Sai dai Julian Alvarez ne ya ramawa City kuma bata tsaya nan inda ta kara zura kwallaye uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ta hannun Kevin De Bruyne da Ilkay Gundogan da Jack Grealish.
A cikin minti na 17 da take wasa, Liverpool zura wa City kwallo ta hannun Mo Sallah.
To amma a minti na 27, Julian Alvarez – wanda ya fara wasan a madadin Erling Haaland – ya farke wa City, bayan Jack Grealish ya bugokwallon ta gefe.
A cikin dakika 53 bayan komawa hutun rabin lokaci ne kuma, Kevin De Bruyne ya zura kwallo ta biyu, lokacin da Mahrez ya kwaso masa wata kwallo
Ana minti na 53 kuma, Ikay Gündogan ya kara ta uku, bayan ya tsinci kwallon da Alvarez ya buga a da’irar yadi na 18.
Kafin daga bisani Jack Grealish – wanda ya kasance gwarzon dan wasa a karawar – ya zura tasa kwallon bayan Kevin De Bruyne ya yi masa daga buhu sai tukunya.