Manchester City na bukatar cin wasa daya nan gaba ta lashe Firimiyar Ingila, bayan da ta doke Everton 3-0 a wasan mako na 36 ranar Lahadi.
Minti na 37 da take leda Ilkay Gundogan ya ci kwallo, kuma minti biyu tsakani Erling Haaland ya kara na biyu, kuma Gundogan ne ya saka masa tamaular.
- Haaland ya zama dan kwallon da babu kamarsa a Firimiyar Ingila a bana
- Angola ta zarce Najeriya a hako danyen man fetur —OPEC
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Gundogan ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a karawar ta Goodison Park.
Karo na biyu kenan da Gundogan ya zura biyu a raga ya kuma bayar aka ci a Premier tun bayan Oktoban 2016 a fafatawa da West Brom.
Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama na neman maki uku kacal a karawa ukun da suka rage mata da za ta yi da Chelsea da Brighton da kuma Brentford.
An kawo wannan kadami ne bayan Arsenal mai maki 81 da ta matse wa City lamba ta sha kashi har gida a hannun Brighton.
A halin yanzu dai wasanni biyu suka rage wa Arsenal a Firimiyar bana, yayin da kuwa City mai maki 83 tana da ragowar biyu da kuma kwantai guda.
Rashin nasara da Everton ta yi ya sa ta koma ta 17 da tazarar maki daya tsakaninta da Leeds, wadda take ‘yan ukun karshen teburi.