✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Angola ta zarce Najeriya a hako danyen man fetur —OPEC

OPEC ta ce an samu raguwar hako man fetur a Iraq da Najeriya.

Adadin danyen man da Najeriya ke hakowa ya ragu zuwa ganga dubu dari 9 da 99 a kowace rana a watan Afrilu.

Wannan lamarin dai ya sa yanzu Angola ta shiga gaban Najeriya saboda tana samar da ganga miliyan 1 da 63 a kowace rana.

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton wata wata na watan Afrilu da kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai ta fitar a karshen makon da ya gabata.

Najeriya ta yi asarar gangunan danyen mai dubu 270 a watan Maris, kamar yadda alkalumman kungiyar OPEC din suka nuna.

OPEC ta ce gaba daya, mambobinta 13 na samar da gangunan mai miliyan 28 da dubu 60 a kowace rana a cikin watan da aka yi la’akari da shi wajen yin wannan rahoto.

Ta ce an samu karuwar danyen man da ake samarwa a Saudiyya, Angola da Iran, a yayin da aka samu akasin haka a Iraq da Najeriya.