✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan —NIDCOM

Jimillar mutanen da Gwamnatin Tarayya ta kwaso sun kai 2,518.

Hukumar da ke kula da ’yan Najeriya mazauna ketare NIDCOM, ta ce an kammala jigilar kwaso ‘yan kasar da suka makale a Sudan da ke fama da rikici.

Hakan na kunshe ne cikin wani sako da hukumar ta NIDCOM ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar.

“A ranar Asabar 13 ga watan Mayu, jirgin Tarco Air ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da misalin karfe 8:30 na dare a Abuja, dauke da mutum 147.”

Sanarwar ta kara da cewa an kwaso fasinjojin karshen ne daga filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Port Sudan.

“Wannan zangon fasinjoji na karshe shi ne na 15, wanda hakan ya kai jimullar mutanen da Gwamnatin Tarayya ta kwaso zuwa 2,518” a cewar NIDCOM.

“Babu ran dan Najeriya ko daya da ya salwanta ya zuwa yanzu a Sudan” a cewar NIDCOM.

A ranar 15 ga watan Afrilu fada ya barke tsakanin sojoji da dakaru na musamman (RSF).

Daruruwan mutane sun mutu yayin da dubbai suka jikkata.

Mutum dubu 200 sun tsere daga Sudan —MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce kimanin mutane dubu 200 ne suka tsere daga Sudan don kauce wa yakin da ya barke a tsakiyar watan Afrilu, kari a kan daruruwan dubbai da yakin ya daidaita a cikin kasar.

Kakakin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar, Olga Sarrado ta shaida wa manema labarai a Geneva cewa karin mutane na tsallakawa zuwa wasu kasashe daga Sudan a kullum saboda wannan rikici.

Tun da farko a wannan mako, Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta ce sama da mutane dubu 700 ne wannan yaki ya daidaita a cikin kasartun da wanna yaki ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu.

Yakin ya yi sanadin mutuwar mutane 750 tare da jikkata sama da dubu 5.

Bangarorin da ke rikici ba su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba, amma sun sha alwashin bai wa fararen hula kariya, tare da barin kayayyakin agajin da ake bukata su shiga kasar.

Jakadan MDD a Sudan, Volker Perthes ya ce amincewa kayyakin agaji su shiga kasar abu ne mai mahimmanci, duba da yadda za a bi dokokin Majalisar Dinkin Duniya.