✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

City da United za su yi karon batta a wasan ƙarshe na Kofin FA

Shi ne kofi daya tilo da United ke da fata a kai na ganin ta kai labari wajen lashe shi.

Kungiyoyin kwallon kafa na Manchester City da Manchester United sun shirya karon batta da juna a gobe Asabar a wasan karshe na cin kofin FA.

Wannan dai shi ne kofi daya tilo da United ke da fata a kai na ganin ta kai labari wajen lashe shi a wannan kaka.

Karawar wadda za ta gudana a filin wasa na Wembley a gobe Asabar, na zuwa ne a wani yanayi da Manchester United ke harin kofin na FA karon farko bayan wanda ta lashe a 2016 karkashin jagorancin Jose Maourinho.

Samun wannan kofi zai karfafa gwiwar tawagar daidai lokacin sabon mamallakinta, Sir Jim Ratcliffe ke shirin aiwatar da sabbin tsare-tsaren da ya ke ganin za su dawo da kungiyar kan turba daga mummunan koma bayan da ta samu.

United za ta doka wasan cike da sanin cewa rashin nasara a hannun City na shirin tabbatar da yiwuwar rashin samun damar haskawarta a Turai cikin kaka mai zuwa, wanda zai zama karo na biyu da kungiyar ta tsinci kanta a irin wannan yanayi tun bayan kakar wasa ta 1982, inbanda shekaru 5 lokacin da dukkanin kungiyoyin Ingila suka fuskanci haramcin haskawa a gasar ta Turai.

United dai ta kammala firimiyar bana ne a matsayin ta 8 mataki guda kasa da yadda ta tsinci kanta a kakar wasa ta 2014 karkashin David Moyes, haka zalika mataki mafi kaskanci tun 1990.

Duk da yadda haduwar ta gobe ke da matukar muhimmanci kuma cike da tarihi, masana na ganin abu ne mai wuya tawagar ta Erik ten Hag ta iya kai bantenta a hannun yaran Pep Guardiola.