✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Gombe za ta raba kayan abinci karo na 2

A baya gwamnatin ta raba wa magidanta 420,000 kayan abinci.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, zai kaddamar da rabon tallafin kayan abinci karo na biyu a fadin jihar.

Yahaya, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a jawabinsa na sabuwar shekarar 2024, inda ya ce za a fara rabon a ranar Talata, ga magidanta 90,000.

A baya gwamnatin jihar ta tallafa wa magidanta 420,000 da kayan abinci daban-daban.

A cewarsa “A wannan karon wadanda za su ci gajiyar tallafin kayan abincin har da kungiyar kwadago (NLC) da kuma kungiyar ‘yan jarida wadanda da su ake yin gwagwarmaya wajen yayata ayyukan gwamnati amma ba su samu tallafin a karon farko ba.”

Ya kuma nemi hadin kan al’umma wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

Gwamnan ya yi fatan shekarar 2024 da aka shiga ta zama shekara mai cike da nasarori ba kalubale kamar ta 2023 ba.