Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce yana sane da halin kuncin da ’yan Najeriya ke ciki sanadiyyar janye tallafin man fetur, amma tallafin rage radadi na nan tafe.
Ya ce an cire tallafin ne domin amfanin ’yan kasa, kuma nan ba da jimawa ba za su fara cewa sambarka da daukar matakin.
- An kori dan majalisa yayin zama saboda yin shigar da ba ta dace ba
- An sake dawo da ’yan ci-ranin Najeriya 146 da ke gararamba a Nijar
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tsofaffin Gwamnonin Najeriya su 18 da suka yi mulki tare a shekara ta 1999, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Tinubu ya bayar da tabbacin cewa yanzu haka suna can sun dukufa aikin fito da hanyoyin tallafa wa ’yan kasa hanyoyin rage radadin, musamman ta fannin bayar da kudade.
A cewarsa, “Na fahimci mutanenmu na cikin wahala, amma duk da haka, sai an sha wuya akan sha dadi. Yanzu haka Najeriya ta bude sabon shafi tun bayan janye tallafin.
“Wannan wani yunkuri ne na ’yantar da mafiya yawan mutane daga wasu tsirarun ’yan fasakwauri. Ku ce da mutane su dan kara hakuri kadan. Tallafin rage radadi na na tafe nan ba da jimawa ba.
“Ba na son kudaden tallafin da za mu bayar su fada hannuwan da ba su dace ba. Na san akwai wahala sosai, amma daga karshe za mu ji dadi mu ce gwamma da aka yi,” kamar yadda ya shaida wa tsofaffin takwarorin nasa, wadanda tsohon Gwamnan Edo, Lucky Igbinedion.
Tun da farko dai Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai wasika yana bukatar su amince masa ya kashe Naira biliyan 500 domin samar da abubuwan rage radadin.
Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ne ya karanta wasikar a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Ya ce bukatar ta zama wajibi saboda a ba gwamnati damar samar da kayan tallafin ga ’yan Najeriya domin rage radadin.