✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake dawo da ’yan ci-ranin Najeriya 146 da ke gararamba a Nijar

Mutanen sun shiga kasar ne da niyyar wucewa Turai

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), a ranar Laraba ta karbi wasu ’yan Najeriya 146 da suke makale kuma suke gararamba a Niamey, Jamhuriyar Nijar.

Ko’odinetan hukumar a ofishinta na Kano, Dokta Nuraddeen Abdullahi, ne ya bayyana hakan lokacin da yake karbar mutanen a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa mutanen sun isa Kano ne wajen misalin karfe 10:35 na safiyar Laraba a jirgin B737-400 SKY MALI mai lamba UR-CQX.

Dokta Nuraddeen ya ce an dawo da su ne a karkashi shirin dawo da mutane bisa radin kansu, wanda Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya take kula da shi.

Ya ce an kirkiro shirin ne da nufin dawo da ’yan Najeriyar da suka bar kasar da nufin ci-rani a kasashen Turai, amma suka makale a hanya kuma ba su da kudin dawowa gida.

Ya ce, “Mutanen sun hada da maza 56 da mata 39, kuma sun fito ne daga sassa daban-daban na jihohin kasa musamman Katsina, Kano, Adamawa, Legas, Imo, Enugu, Edo da sauransu.

“Za a ba mutanen horo na tsawon kwanaki uku kan yadda za su koma dogaro da kansu, kafin daga bisani a ba su jari domin su dogara da kansu,” in ji shi.

Ko’odinetan ya kuma shawarci jama’a da su kiyayi jefa rayuwarsu cikin hatsari ta hanyar neman ingantacciyar rayuwa a kasashen waje, bayan za su iya samun ta a gida.

“Babu wata kasa da ta fi Najeriya da za mu je mu samu ingantacciyar rayuwa kuma mu zauna cikin farin ciki sama da Najeriya,” in ji shi. (NAN)