Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 339 na cin zarafi a Jihar Gombe a shekarar 2024.
Kakakin hukumar, Mista Ali Alola-Alfinti, ya ce mafi yawan shari’o’in sun shafi tauye haƙƙin iyaye.
- Tinubu ya ɗage gabatar da kasafin kuɗin 2025 zuwa Laraba
- Hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 34.60 a Nuwamba — NBS
Ya ce maza na barin matansu da ’ya’yansu ba tare da kula ba, inda suke amfani da talauci da matsin tattalin arziƙi a matsayin hujja.
“Yawan ƙorafe-ƙorafen ya ƙaru ne saboda ci gaba da wayar da kan jama’a game da cin zarafin haƙƙin ɗan adam,” in ji shi.
Ya ce hukumar na aiki tare da ƙungiyoyin masu zaman kansu, kafafen watsa labarai, da shugabannin addinai don ilmantar da al’umma da ƙarfafa musu gwiwa don kawo rahoton cin zarafin.
“Yanzu mutane da dama suna kai rahoto, kuma hakan yana taimakawa wajen yaƙi da cin zarafin haƙƙin ɗan adam,” in ji Alola-Alfinti.
“Yin shiru shi ne babbar matsala, domin ba za a iya kare haƙƙi ba idan ba a sanar da matsalar ba.”
Ya ƙara da cewa kusan kashi 50 cikin 100 na ƙorafe-ƙorafen suna da alaƙa da tauye haƙƙin iyaye, musamman barin iyali ba tare da abinci, tufafi, ko wajen zama ba.
“Hukumar ta ƙarfafa wa jama’a gwiwa don magance matsalar, ta kuma yi kira ga maza da su kula da iyalansu,” in ji shi.