Ma’aikatan majalisun dokokin jihohi da ke fadin Najeriya sun yi barazanar fara yajin aiki daga ranar Laraba.
Ƙungiya Ma’aikatan Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (PASAN) ta ce za ta tsunduma yajin aikin ne saboda kin ba wa majalisu ’yancin gudanar da kuɗaɗensu da gwamnoni suka yi.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ya Hana Farashin Dala Sauka
- An kama masu yunƙurin daura auren jinsi a Gombe
Ƙungiyar ta sanar cewa mambobinta za su daina aiki su kuma rufe ofisoshinsu, har sai gwamnoni sun gaggauta ba wa majilisun ’yancin gudanar da kuɗaɗensu.
Sakatare-Janar ta PASAN, Agugbue Ugochi Happiness, ta ce wajibi ne gwamnoni su ba wa majalisun jihohi ’yancin cin gashin kansu da gudanar da kuɗaɗensu kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ta bayyana cewa za su shiga yajin aikin ne bayan cikar mako guda suka kara a bisa wa’adin mako uku da suka fara ba wa gwamnoni na yin abin da ya dace, wanda ya kare tun ranar 18 ga watan Satumbam 2023.
Sanarwar yajin aikin da ta aike wa Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) da Hukumar Tsaro ta DSS da kuma Ƙungiyar Shugabannin Majalisun Dokoki, ta bayyana cewa shiga yakin aikin ta zama dole, idan sabon wa’adin ya cika gwamnonin ba su yi abin a zo a gani ba kan lamarin.
Ma’aikatan Majalisun dai sun sha gudanar da zanga-zanga domin ganin majalisu sun samu ’yancin gashin kansu, amma hajar ba ta cim-ma ruwa ba.
“Muna fata za su yi amfani da karin wa’adin su yi abin da ya kamata, su biya mana bukatunmu, ida ba haka ba za mu umarci mambobinmu su fara yajin aikin,” in ji ta.