✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cikin ‘’yan sa’o’i’ za mu ceto daliban Katsina —Ministan Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ce ta shirya tsaf domin kubutar da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara da ’yan bindiga suka kai wa hari ranar Juma’a da…

Gwamnatin Tarayya ta ce ta shirya tsaf domin kubutar da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara da ’yan bindiga suka kai wa hari ranar Juma’a da dare.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi ne ya bayar da tabbacin bayan Gwamna Aminu Bello Masari ya shaida masa cewa dalibai 333 ne suka bace bayan harin.

Magashi wanda ya kai ziyarar jaje ga jihar tare da Manyan Hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro ya ce nan da ’yan sa’o’i za a kwato daliban cikin sauki kuma koshin lafiya.

Ministan tsaron, wanda ya la’anci harin, ya ce lokaci ya yi na Gwamnatin Tarayya ta ayyana ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda domin hakan zai sa a tashi tsaye wurin yakar su.

Magashi ya ce tuni hukumomin tsaro suka fara aiki, kuma sun riga sun tsara yadda aikin ce daliban zai kasance ta hanyar amfani da bayanan sirrin da suka riga suka tattara.