Jami’an tsaron hadin gwiwa sun ceto mutane 24, ciki har da dalibai da malamai da ’yan bindiga suka sace a Jihar Kogi, cikin kasa da awa 24.
A ranar Asabar ne hadin gwiwar ’yan sanda da ’yan banga da sojoji suka ceto mutanen da aka sace su ranar Juma’a, a yankin Adogo na Karamar Hukumar Ajaokuta da ke jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya ce akwai dalibai 11 da malamai uku a cikin wadanda aka yi garkuwa da sun da aka kubutar.
Jami’in ya bayyana cewa a yayin musayar wuta a samame da aka kai maboyar ’yan bindigar ne suka tsere suka bar mutanen da ke hannunsu.
- Kanin mahaifin Abba Gida-gida ya rasu
- Kano da Bauchi sun lashe Gasar Alkur’ani ta Kasa ta 2023
- Harin Filato: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro
Sanarwar da ya fitar ta ce, “A lokacin da rundunar ke sharar dajin domin neman mutanen ne ’yan ta’addan suka hango su daga maboyarsu, suka bude wa tawagar wuta.
“A yayin artabu ne ’yan bindigar suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.”