✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanin mahaifin Abba Gida-gida ya rasu

Marigayi Dan’makwayo, wanda jami’in jinya mai ritaya ne, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa kanin mahaifin Gwamna Abba Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, Alhaji Hassan Yusuf Danmakwayo rasuwa.

Marigayi Dan’makwayo, wanda jami’in jinya mai ritaya ne, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar cewa marigayin ya rasu ne a ranar Asabar kuma tuni aka yi jana’izarsa yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sanusi Bature ya ce Marigayin ya rasu ya bar matarsa ​​da ’ya’ya da dama da jikoki da ’yan uwa.

Gwamna Abba yi addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya sa Jannatul Firdaus ce makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin rashin.